Yan sanda sun kama manyan yan fashi 4 a Abuja
- Jami'an yan sanda sun kama wasu yan fashi hudu a Abuja
- Yan fashin kan badda kamanni a matsayin masu motar haya da fasinja, sai su karkatar da fasinjojin bayan dan tafiya mai tsawo sannan su yi masu fashin kayayyakinsu
- Bayan sun yiwa mutane fashi sai kuma su yasar da su waje alhalin motar na cikin tafiya
Rundunar yan sandan Abuja sun kama wasu yan fashi hudu a babbar birnin tarayyar kasar.
Daily Trust ta ruwaito cewa yan fashin kan badda kamanni a matsayin masu motar haya da fasinja, sai su karkatar da fasinjojin bayan dan tafiya mai tsawo sannan su yi masu fashin kayayyakinsu sai kuma su kora su daga cikin motar.

Asali: Depositphotos
Kakakin rundunar, DSP Anjuguri Manzah, a wata sanarwa da ya saki a jiya, yace jami’an rundunar da ke yaki da yan fashi sun kama wani Onyebuchi Ifeanyikwu, dan shekara 40, da Anthony Sunday, mai shekara 35, a mabuyarsu da ke Tungan Maje a ranar 10 ga watan Nuwamba bayan bincike.
KU KARANTA KUMA: Sauya shekar yan majalisa: APC na fafutukar ganin ta ci gaba da kasancewa mafi rinjaye
“Masu laifin sun yi wa wata mata da ta hau motarsu fashi har suka ji mata rauni a hanyar Nyanya daga Arab Kubwa a ranar 9 ga watan Nuwamba. Jim kadan bayan sun dauki hanya sai suka karkatar da motar zuwa hanyar Zuba inda suka yi mata fashin kudade, waya da katin ATM biyu da sauran abubuwa masu muhimmanci kafin suka yasar da ita,” inji shi.
Manzah ya kara da cewa rundunar sun kuma kama wani Usman Ali da Sani Bala yan shekara 19 wanda aka zarga da yin fashi a daidaita sahu a ranar 2 ga watan Nuwamba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng