An sallami jami’in dan sandan da ya sha giya ya bugu a cikin wani bidiyo (hoto)
Rundunar yan sandan Najeriya ta sallami jami’in ta da aka dauka a wani bidiyo bayan ya sha giya ya bugu.
Bidiyon wanda ya yi fice sannan ya ke nuna jami’in dan sanda daga yankin Akowonjo, Dopemu da ke jihar Lagas ya ja hankalin babban sugfeto na yan sanda Ibrahim Idris.
Don haka ya umurci kwamishinan yan sandan jihar, CP Imohimi Edgal da ya tsamo dan sandan sannan a ladabtar da shi.
An gurfanar da dan sandan a yau Laraba, 7 ga watan Nuwamba a sashin Ikeja inda yake aiki. Sannan an bayyana sunanasa a matsayin KadimaUseni tare da lambar daukar aiki 176219.

Asali: Facebook
A lokacin bincike, jami’in ya tabbatar da cewar shine a bidiyon don haka sallame shi domin ya zama izina ga sauran mutane.
Sannan an gargadi jami’an yan sanda kan shan giya a yayinda suke bakin aiki. Cewa daga yanzu duk wanda aka kama toh za’a sallame shi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng