Wani matashi ya fado daga Falwaya wajen lika hotunan Buhari da Badaru a Jigawa
Labari da ke zuwa mana ya nuna cewa wutar lantarki ya yi sanadiyar mutuwar wani matashi da aka ambata da suna Jamilu Tukur a wani kauye mai suna Kudai da ke karamar hukumar Dutse, babbar birnn jihar Jigawa.
Premium Times ta ruwaito cewa kakakin yan sandan jihar, Audu Jingiri ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba, 14 ga watan Nuwamba.
Jingiri ya bayyana cewa Jamilu dan shekara 27 ya mutu ne a ranar Asabar bayan ya hau saman falwaya domin lika hotunan shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Mohammad Badaru.

Asali: Instagram
Wani mazaunin kauyen Kudai mai suna Nasiru Sani ne ya sanar wa ‘yan sanda rasuwar Jamilu.
“Ya bayyana mana cewa garin manna wannan fosta ne ya kama wayar wutar lantarki kuma a nan take ko ya fado kasa. An yi kokari kai shi asibiti cikin gaggawa a Dutse amma kafin a iya wani abu yace ga garinku nan."
KU KARANTA KUMA: Buhari ya dawo Abuja bayan ziyarar kwanaki 5 da ya kai Paris (hotuna)
Da yake juyayin mutuwar babbar dansa, mahaifin Jamilu, Tukur yace wannan kaddara ce daga wajen Allah. Ya ce dan sa yaro ne mai hankali da kirkin gaske.
A karshe Tukur ya mika godiyyar sa na musamman ga gwamna Badaru da karamar hukumar Dutse bisa ta’aziyya da suka yi masa da kyaututtuka na kudi da abinci da suka bashi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng