Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
A yau Asabar, 8 ga watan Yuni ne, tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, Janar Sani Abacha ya cika shekaru 21 da mutuwa. An haifi Janar Sani Abacha ranar 20 ga watan Satumbar shekarar 1943 a cikin garin Kano.
Akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa rikici tsakanin gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya zo karshe biyo bayan wata matsaya da aka cimma a daren ranar Juma’a a Abuja.
A kwanan nan ne aka yi bikinwani mutumi mai suna Kabiru Mohammed Garkuwa a garin Jos inda ya auri santala-santala yan mata guda biyu a rana daya.
Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Aminu Waziri tambuwal ya nada Ubandoman Sokoto, Hon. Saidu Umar a matsayin babban Sakataren gwamnatin jihar. Umar ya kasance tsohon kawmishinan kudi na jihar.
Fadar shugaban kasa ta bayyana matsayarta akan lamuran da suka shafi sabbin kudaden da aka gano daga cikin kudaden da tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Sani Abacha ya karkatar.
Rundunar yan sanda a jihar Bauchi sun kama wasu mutane hudu da ake zargin yan fashi da makami ne da kuma yan Sara-Suka 60 a fadin jihar. An gurfanar da masu laifin ne a hedkwatar rundunar da ke Bauchi.
A zamanin da muke ciki kiba ya zamo abun ki a tsakanin al’umman musamman mata domin a ganinsu yana rage masu kyawu da sauran jin dadin rayuwa.
Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ya amince da nadin Alhaji Abdullahi Gashua a matsayin Shugaban ma’aikatansa. Nadin zai fara aiki ne ba tare da bata lokaci ba.
Mazauna garin Maiduguri, babbar birnin jihar Maduguri a jiya, Talata, 4 ga watan Yuni sun yi bikin karamar Sallah cikin kwanciyar hankali da lumana.
Aisha Musa
Samu kari