Kudin Abacha: Gwamnatin tarayya ta bayyana abunda za ta yi da sabon $300m da aka gano

Kudin Abacha: Gwamnatin tarayya ta bayyana abunda za ta yi da sabon $300m da aka gano

- Fadar shugaban kasa ta karyata rahotanni dake cewa za ayi rabon wasu kudaden da marigayi, Janar Sani Abacha ya karkatar a tsakanin kasashen Amurka, Jersey da Najeriya.

- Hadimar shugaban kasa, Juliet Ibekaku-Nwagwu, a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli ta bayyana cewa kudaden na Najeriya ne

- Nwagwu har ila yau ta bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace za ayi amfani da kudaden wajen gudanar da ayyukan da zai amfani al’umma idan aka kammala tattaunawa

Fadar shugaban kasa ta bayyana matsayarta akan lamuran da suka shafi sabbin kudaden da aka gano daga cikin kudaden da tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Sani Abacha ya karkatar.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Juliet Ibekaku-Nwagwu, Hadimar Shugaban kasa ta bayyana cewa adadin kudaden da aka rahoto cewa ya kai kimanin £210 million wanda yayi daidai da dala miliyan 267 ko naira biliyan 82 ba daidai bane.

Nwagwu, a lokacin da take karyata ikirarin cewa za ayi rabon kudaden tsakanin Najeriya, Amurka da Jersey, ta dage cewa kudin na Kasar Najeriya ne kuma za a kammala tattauana akan yanda za a aiwatar da ayyuka da kudin ta yanda al’umma zasu amfana.

A halin da ae ciki, Legit.ng ta rahoto cewa Najeriya, Amurka da Jersey a Birtaniya za su yi rabon £210 million na Abacha. A 2014 ne kamfanin Shell Compay wacce aka fi sani da Doraville ta daskarar da kudin.

KU KARANTA KUMA: Hawan Sallah: Yan sanda sun kama yan daba 10 a Kano

Bayan an share shekaru biyar ana musu akan lamarin da ya shafi kudin, kudin ya fito kuma za a raba tsakanin Jersey, Amurka da Najeriya. Har ila yau dai ba a bayyana nawa kowace gwamati zata samu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel