Magana Ta Ƙare: Kotu Ta Shirya Yanke Hukunci kan Karar da Aka Shigar da Pantami
- Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta gama zama game da hukunci kan karar da Usman Garry ya shigar domin kalubalantar tsayar da Farfesa Isa Pantami
- Garry ya ce Pantami bai cikin kundin rajistar mambobin PDP da aka mika wa INEC kafin wa'adin 10 ga Mayun 2026, saboda haka bai cancanci shiga zaben fidda gwani ba
- Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Pantami, ya samu damar shiga sabon zaben fitar da gwani da PDP ta gudanar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta tanadi hukunci kan karar da dan jam'iyyar PDP a Gombe, Usman Garry, ya shigar.
Garry yana kalubalantar sahihancin tsayar da tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, a matsayin dan takarar gwamnan jihar a zaben 2027.
A zaman kotun da aka ci gaba da sauraren karar a ranar Laraba, lauyoyin bangarorin biyu sun gabatar da hujjojinsu tare da yin bayanan karshe, kafin alkalai su ajiye hukuncin zuwa wani lokaci, cewar Premium Times.
Garry ya daukaka kara ne kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya na ranar 24 ga Satumban 2026, wadda ta soke zaben fidda gwani na PDP da aka gudanar a ranar 26 ga Mayu, tare da umartar jam'iyyar ta sake gudanar da sabon zabe.
Sai dai kotun ta ki amincewa da bukatar hana Pantami shiga sabon zaben fidda gwani.
A karar da ya shigar, Garry ya kalubalanci cancantar Pantami bisa tanadin sashe na 77 na dokar zabe ta 2026.
Ya bayyana cewa ba a saka sunan Pantami cikin kundin rajistar mambobin PDP da aka mika wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) kafin wa'adin doka na ranar 10 ga Mayun 2026 ba.
Garry ya kara da cewa Pantami ya koma PDP ne a ranar 19 ga Mayu, kwanaki tara bayan wa'adin da doka ta tanada, don haka bai cancanci shiga zaben fidda gwani ba.
Saboda haka, ya bukaci Kotun Daukaka Kara ta soke bangaren hukuncin da ya ba Pantami damar shiga sabon zaben fidda gwani tare da amincewa da bukatun da ya gabatar a karar farko.
Yanzu haka, Kotun Daukaka Kara za ta yanke hukunci kan ko Babbar Kotun Tarayya ta yi kuskure wajen bai wa Pantami damar shiga sabon zaben fidda gwani na ranar 29 ga Satumban 2026, duk da cewa bai cikin kundin rajistar mambobin jam'iyyar da aka rufe a ranar 10 ga Mayu.
Karin bayani na tafe ....
Asali: Legit.ng

