Gwamna Ya Karbi Rahoton Abubuwan da Aka Gano kan Mutuwar Matasa 37 a Ofishin NSCDC

Gwamna Ya Karbi Rahoton Abubuwan da Aka Gano kan Mutuwar Matasa 37 a Ofishin NSCDC

  • Gwamna Mohammed Umaru Bago ya karɓi rahoton kwamitin bincike kan mutuwar masu haƙar ma’adinai 37 a hannun hukumar NSCDC
  • Shugaban kwamitin, Mai Shari’a Muhammad Muhammad, ya ce sun karɓi takardun ƙorafe-ƙorafe guda tara tare da sauraron shaidu da dama
  • Bago ya ce zai tura kwafin rahoton zuwa Fadar Shugaban Ƙasa domin samun kulawa da kuma aiwatar da shawarwarin da ke cikinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya karɓi rahoton kwamitin binciken da aka kafa domin binciko musabbabin mutuwar masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba guda 37.

Matasan sun rasa rayukansu a hannun hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC), reshen jihar Neja bayan an kama su bisa zargin hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba.

Gwamna Bago.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago a fadar gwamnati da ke Minna Hoto: Umaru Mohammed Bago
Source: Facebook

Leadership ta ruiwaito cewa shugaban kwamitin, Mai Shari’a Muhammad Muhammad, ne ya jagoranci sauran mambobin kwamitin zuwa gidan gwamnatin jihar da ke Minna, inda suka miƙa rahoton ga gwamnan.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Neja ta tabbatar da kashe mutum kusan 100 a jihar

Gwamna Bago ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na bin shawarwarin da kwamitin ya bayar tare da tabbatar da an aiwatar da su.

Ya bayyana cewa rahoton zai zama muhimmin jagora ga hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki da abin ya shafa.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa za a aika da kwafin rahoton zuwa Fadar Shugaban Ƙasa domin ta yi amfani da shi wajen duba lamarin.

Ya ce har yanzu gwamnatin tarayya ba ta aiwatar da shawarwarin kwamitin da ta kafa domin binciken mutuwar masu haƙar ma’adinan 37 ba.

Yadda aka gudanar da binciken

Rahoton ya nuna cewa masu haƙar ma’adinai 37 sun mutu ne a hannun hukumar NSCDC ranar 17 ga watan Satumba, 2026. Lamarin ya sa gwamnatin jihar Neja ta kafa kwamitin bincike domin gano yanayin da ya kai ga mutuwarsu.

Kwamitin ya gayyaci shaidu sama da 50 domin su bayar da bayanai kan lamarin. Daga cikin waɗanda aka gayyata akwai kwamandan NSCDC na jihar Neja da aka dakatar, Siaka Suberu Aniviye.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya tube babbar riga ya tafi kotu kare El Rufa'i

Yayin gabatar da rahoton, Mai Shari’a Muhammad ya ce kwamitin ya karɓi takardun ƙorafe-ƙorafe guda tara, ya gudanar da zaman sauraron ra’ayoyin jama’a, sannan ya kai ziyara wurare daban-daban domin tattara bayanai.

Ya ce kwamitin ya duba wuraren haƙar ma’adinai guda biyu, ofisoshin NSCDC guda biyu da kuma babban asibitin Minna.

Shaidu sun taimaka wajen yanke hukunci

Muhammad ya ce bayanan da aka tattara daga shaidu yayin zaman sauraron ƙorafe-ƙorafen jama’a su ne suka zama tushen binciken kwamitin, tare da taimaka masa wajen gano abubuwan da suka faru da kuma tsara shawarwarin da ya gabatar.

Sai dai rahoton da aka gabatar bai bayyana dalla-dalla irin shawarwarin da kwamitin ya bayar ba.

Kun ji cewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262