Gwamnan jihar Yobe ya nada Shugaban ma’aikata

Gwamnan jihar Yobe ya nada Shugaban ma’aikata

- Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ya nada sabon Shugaban ma’aikatansa

- Mai Mala ya amince da Alhaji Abdullahi Gashua domin ya 'dare wannan matsayi

- Sakataren labaran gwamnatin jihar, Shuaibu Abdullahi, ya bayyana hakan a jiya Talata, 4 ga watan Yuni

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ya amince da nadin Alhaji Abdullahi Gashua a matsayin Shugaban ma’aikatansa.

A cewar wani jawabi daga sakataren labaran gwamnatin jihar, Shuaibu Abdullahi, a jiya Talata, 4 ga watan Yuni ya bayyana cewa nadin zai fara aiki ne ba tare da bata lokaci ba.

Kafin nadin nasa, Gashua ya kasance daraktan gudanarwa na hedkwatar jam’iyyar All Progressives Congress.

KU KARANTA KUMA: Alhamdulillah: Al’umman Maiduguri sun yi bikin karamar sallah cikin kwanciyar hankali

A wani labari na daban, mun ji cewa Gwamnatin jahar Yobe a karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ta sanar da dakatar da zirga zirgan ababen hawa a ciki da wajen garin Damaturu tun daga karfe 10 na daren Litinin zuwa karfe 10:30 na safiyar Talata.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin gwamnan jahar, Abdullahi Bego ne ya bayyana haka a daren Litinin, inda yace Gwamnan jahar ya dauki wannan mataki ne bayan ganawa da shuwagabannin hukumomin tsaro dake jahar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel