Majalisar Kaduna: Dan takarar gwamnati mai shekaru 39 ya lashe zaben kakakin majalisa

Majalisar Kaduna: Dan takarar gwamnati mai shekaru 39 ya lashe zaben kakakin majalisa

Majalisan dokokin jihar Kaduna ta sake zabar Aminu Abdullahi Shagali a matsayin kakakinta a majalisa na shida da aka fara a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni.

Da farko an zabi Aminu Shagali dan shekara 39 a majalisar jihar a 2011 domin wakiltan mazabar Sabon Gari.

Ya zama kakakin majalisar a 2015 bayan nasara da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tayi a matsayin jam’iyyar siyasa mai mulki a jihar.

Sake zaben Shagali da aka yi bai zo da mamaki ba, kamar yanda shugaban jam’iyya mai mulki na All Progressives Congress a jihar, Gwamna El-Rufai ya bayyana dawowarsa a matsayin kakakin majalisa.

Gwamna El-Rufai jim kadan bayan sake zabensa ya bukaci yan majalisar da su ci gaba da mara wa shugabancin majalisan baya, wanda yace tayi aiki gwargwado tare da majalisar zartarwa don cika alkawarin gwamnati ga mutanen jihar Kaduna.

KU KARANTA KUMA: An shiga rudani bayan likitar bogi ta sace jaririya yar kwana 3 daga asibitin Plateau

A wani labari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Hon. Amin Achida (APC/Wurno) ya zama sabon kakakin majalisar dokokin jihar Sokoto a ranar Talata, 11 ga waan Yuni, a taron rantsar da majalisar dokokin na tara.

Achida ya kayar da dan takarar da jam’iyyarsa ta APC ta tursasa wato Abdullahi Garba Sidi, mai wakiltan yankin Gwadabawa ta kudu.

Zababbu mambobin majalisa 30 karkashin jagorancin mukaddashin magatakardar majalisar dokokin jihar, Alhaji Abdulrazak Shehu ne suka gudanar da zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel