'Yan sanda sun kama wasu rikakkun 'yan fashi guda 4 da yan daba 60 da suka addabi jihar Bauchi

'Yan sanda sun kama wasu rikakkun 'yan fashi guda 4 da yan daba 60 da suka addabi jihar Bauchi

Rundunar yan sanda a jihar Bauchi sun kama wasu mutane hudu da ake zargin yan fashi da makami ne da kuma yan Sara-Suka 60 a fadin jihar. An gurfanar da masu laifin ne a hedkwatar rundunar da ke Bauchi.

A cewar kakakin yan sandan, DSP Kamal Datti Abubakar, anyi kamun ne duk a cikin kokarin da kwamishinan yan sandan jihar, CP Habu Sani Ahmadu, ke yin a kawar da yan ta’adda a jihar.

Ya bayyana cewa tawagar rundunar na Operations Puff Adder ne suka kama yan fashin ne a ranar 2 ga watan Yuni, 2019.

“Bayan bayanai masu inganci, yan sandan sun kama mutanen Audu Daniel dan shekara 29 na karamar hukumar Gboko, jihar Benue da John Samuel mai shekara 22 na karamar hukumar Orlu, jihar Imo a yankin Kofar Gombe na garin Buachi sannan suka samo mota guda, Lexus Jeep RX 350, 2007 model, kalar ruwan toka, wanda ya kai kimanin naira miliyan hudu.

“Masu laifin sun tona asirin cewa sun yi fashin motar ne tare da wasu a wannan ranar daga wata mata, a daji, hanyar Abuja-Jos,” inji kakakin yan sandan.

Ya bayyana cewa bayan duba motar, yan sandan sun gano wayar Infinix mallakar wacce aka yiwa fashin.

A cewarsa kwafin takardun motar na dauke da sunan Linda Onyinye Anakwe na No. 51 Rukuba Jos, jihar Plateau, kayayyaki, sarkoki da wasu takardu.

KU KARANTA KUMA: Kuka tsakanin karfe 7 zuwa 10 na dare na rage kiba - Bincike

Ya kara da cewa an kama wasu kuma Ikenna Okoronkwo na Janta Adamu, Jos, jihar Plateau da Solomon Ijika na yankin Federal Lowcost a ranar 3 a watan Yuni.

Datti yace a wani mamayar kuma, an kama yan Sara-Suka 60 dauke da wukake biyu, adduna 11 da miyagun kwayoyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel