INEC za Ta Cire Sunan Jam'iyyu a Zaben Gwajin da za Ta Yi a Najeriya

INEC za Ta Cire Sunan Jam'iyyu a Zaben Gwajin da za Ta Yi a Najeriya

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ce ba za a saka sunayen jam’iyyun siyasa a takardun zaɓen gwajin da za a yi a ranar Asabar ba
  • Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce takardun za su kasance na kwaikwayo ne kawai, ba tare da sunayen jam’iyyun siyasa masu rijista ba
  • Ya bayyana cewa za a yi amfani da gwajin wajen tantance ingancin na’urorin BVAS, tsarin tattara bayanai da kuma aika sakamakon zaɓe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ba za a saka sunayen jam’iyyun siyasa masu rijista a takardun zaɓen da za a yi amfani da su a zaben gwaji na ranar Asabar ba.

Kara karanta wannan

'Matsalar da Atiku zai ci karo da ita a yankinsa na Arewa maso Gabas'

Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja, yayin wani taro da kwamishinonin zaɓe na jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya (FCT).

Zaben Ondo na 2026
Mutane a wajen da ake zabe. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa Amupitan ya ce takardun zaɓen za su kasance na kwaikwayo ne, ba na ainihin zaɓe ba, domin guje wa zargin cewa hukumar na ƙoƙarin shirya maguɗi tun kafin zaɓen 2027.

Ba sunan jam’iyyu a zaben gwaji

Shugaban INEC ya ce an fara samun tambayoyi daga jama’a kan ko gwajin na’urar tantance masu zaɓe wata dama ce da hukumar za ta yi amfani da ita wajen shirya maguɗin zaɓe.

Sai dai ya jaddada cewa babu sunan wata jam’iyyar siyasa da zai bayyana a takardun zaɓen da za a yi amfani da su, kuma kowa zai iya tabbatar da hakan.

Ya ce gwajin zai gudana ne a rumfunan zaɓe biyu a kowace mazaba a faɗin ƙasar, domin tantance yadda tsarin hukumar ke aiki a zahiri, ba wai don gudanar da wani biki kawai ba.

Shugaban INEC
Shugaban INEC a wajen taro. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Za a gwada na’urorin BVAS

Amupitan ya bayyana cewa za a yi amfani da gwajin wajen tantance ingancin sababbin na’urorin tantance masu zaɓe na BVAS, tsarin jigilar kayayyakin zaɓe da kuma shafin duba sakamakon zaɓe na INEC (IReV).

Kara karanta wannan

Tinubu ka iya rasa muhimmiya jiha a Arewa kan rigimar gwamna da manyan kasa

Vanguard ta rahoto ya ce hukumar na son gwada yadda ake aika bayanai, tantance su da kuma isar da sakamakon zaɓe ta hanyar fasahar da ta tanada.

A cewarsa, wannan tsari zai taimaka wa jami’an zaɓe wajen tabbatar da cewa sakamakon da suka ɗaura shi ne sahihin sakamakon da aka tantance tare da amincewar waɗanda ke rumfar zaɓe.

An tantance masu zabe a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce ta cire bayanan masu rijistar zaɓe sama da miliyan 1.6 da ba su inganta ba.

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce wannan mataki ya rage adadin masu rijistar zaɓe daga miliyan 103 zuwa sama da miliyan 100.

Amupitan ya bayyana cewa mutane sama da miliyan 10.77 da suka yi sabon rijista sun samu nasarar shiga sahihin kundin masu zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng