Kuka tsakanin karfe 7 zuwa 10 na dare na rage kiba - Bincike

Kuka tsakanin karfe 7 zuwa 10 na dare na rage kiba - Bincike

A zamanin da muke ciki kiba ya zamo abun ki a tsakanin al’umman musamman mata domin a ganinsu yana rage masu kyawu da sauran jin dadin rayuwa.

Sai dai kuma an gano wata hanya mafi sauki da mutum zai bi idon har yana son rage yawan kiba maimakon shan magunguna ko abubuwan da za su zame masa illa.

Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa kuka mai tsuma zuciya na iya taimaka wa mutum wajen rage kiba. Binciken ya nuna cewa hakan na kasancewa ne saboda akwai alaka tsakanin kuka da tantanin halitta da ke taimakawa kan hakan.

Wadanan tantanin halitta zai taimaka wajen rage kiba da zaran mutun sanya abun tausayi a zuciyarsa sannan ya fara kuka.

KU KARANTA KUMA: Alhamdulillah: Al’umman Maiduguri sun yi bikin karamar sallah cikin kwanciyar hankali

Baya ga haka wani masanin fannin gwaje-gwaje Willaim Frey ya gano cewa wahalar da ke tattare da hawaye na iya cire duk wasu abubuwa da ke dauke da guba daga jikin dan Adam. Don haka a lokacin bacin raid a gajiya, jiki kan fitar da wadannan guba ta hanyar kuka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel