'Matsalar da Atiku Zai Ci Karo da Ita a Yankinsa na Arewa maso Gabas'

'Matsalar da Atiku Zai Ci Karo da Ita a Yankinsa na Arewa maso Gabas'

  • Mai ba Shugaba Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai, Daniel Bwala, ya bayyana matsalar da Atiku Abubakar zai fuskanta a yankin Arewa maso Gabas
  • Bwala ya bayyana cewa Tinubu zai doke Atiku da tazara mai yawa a zaɓen 2027, fiye da yadda ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2023
  • Hadimin shugaban ƙasar ya ce yawan mutanen da ke halartar gangamin siyasa ba ya tabbatar da farin jinin ɗan takara ko nasararsa a zaɓe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – Mai ba Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Daniel Bwala, ya yi hasashen zaben 2027

Bwala ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, zai rasa wasu daga cikin ƙuri'un da ya saba samu a Arewa maso Gabas a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Atiku ya sake kifar da Tinubu, ya faɗi yadda zai dawo da tallafi, rage farashin fetur

An yi hasashen Atiku zai rasa Arewa maso Gabas
Shugaba Bola Tinubu da Atiku Abubakar. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Bwala ya yi hasashen zaben 2027 a Arewa

Bwala ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin podcast na Niger Unfiltered, wanda Olawale Oluwade ke gabatarwa, cewar Punch.

Ya ce sauye-sauyen kawancen siyasa da ake samu gabanin zaɓen 2027 na iya rage ƙarfin Atiku a wasu jihohin yankin Arewa maso Gabas, duk da cewa shi ɗan asalin yankin ne.

A cewarsa, Atiku ba zai iya samun nasarar lashe wasu jihohin da ya samu nasara a zaɓukan baya ba.

Bwala ya ce:

“Misali, a Borno, sun yi wa Asiwaju kamfen sosai. Asiwaju ya yi nasara. Zan fi son in bayyana hakan da cewa a Arewa maso Gabas, wanda ni ɗan yankin ne, zai rasa ƙarfi. Waɗancan jihohin da ya lashe, kamar Gombe, ba zai iya lashe su yanzu ba.
“Ba zai iya lashe su yanzu ba.”
Bwala ya ce Tinubu zai doke Atiku
Hadimin Bola Tinubu, Daniel Bwala da Atiku Abubakar. Hoto: Daniel Bwala, Atiku Abubakar.
Source: Facebook

Bwala ya ce Tinubu zai doke Atiku

Kara karanta wannan

Ba boye boye: Tinubu ya fadi kabilar da ya ji haushi ta ki zaben shi a 2023

Bugu da ƙari, hadimin shugaban ƙasar ya nuna kwarin gwiwar cewa Tinubu zai samu ƙarin ƙuri'u a zaɓen 2027, tare da doke Atiku Abubakar da tazara mafi girma fiye da zaɓen 2023.

Ya ce:

“A wannan karon, tazarar da Tinubu zai ba Atiku za ta fi wadda ya ba shi a 2023 nisa sosai.”

Bwala ya yi waɗannan kalaman ne yayin da yake amsa tambayoyi kan yiwuwar Tinubu ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa da kuma ko masu ba shi shawara suna nuna masa yanayin siyasa cikin kyakkyawan fata fiye da gaskiya.

Ya kuma yi watsi da ra'ayin cewa yawan mutanen da ke halartar gangamin jam'iyyun adawa na nuna ƙarfin siyasar 'yan takararsu.

A cewarsa, yawan jama'a a taron siyasa ba hujja ba ce da ke tabbatar da farin jinin ɗan takara, cewar Vanguard.

Ya ce:

“Tun daga farko ni mai fafutukar wannan ra'ayi ne. Ban taɓa sauya matsayina cewa yawan mutanen da ke halartar gangami ba ya tabbatar da farin jini ba.”

Matsalar da Tinubu zai iya fuskanta

An ji labarin cewa Terwase Orbunde ya gargaɗi cewa Shugaba Bola Tinubu na iya rasa gagarumin goyon bayan al'ummar Benue a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya faɗi jihohi 2 da APC za ta iya shan laye a zaɓen shugaban ƙasa na 2027

Dan takarar gwamnan Benue ya zargi Gwamna Hyacinth Alia da kawo cikas ga ƙoƙarin sasanta rikicin.

Orbunde ya buƙaci shugabannin APC na ƙasa su aiwatar da hukuncin kotu, su haɗa kan jam’iyyar tare da tabbatar da dimokuraɗiyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.