Yadda aka yi na auri mata biyu a rana daya - Magidanci

Yadda aka yi na auri mata biyu a rana daya - Magidanci

A kwanan nan ne aka yi bikinwani mutumi mai suna Kabiru Mohammed Garkuwa a garin Jos inda ya auri santala-santala yan mata guda biyu a rana daya.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu akan bikin kasancewar kowace budrwa a wannan zamani so take ace ita kadai ce a wajen maigidanta, gai gashi an samu akasin haka a wajen wadanan ma’aurata.

Yayinda lamarinya birge wasu da dama, wasu na al’ajabin yadda aka yi har mijin ya shawo kan matar suka amince da wannan shirina auransa a rana guda.

Garkuwa dai ya rabu da matarsa ta farko wace suke da haihuwa a tare sama da shekara daya da suka gabata. Anyi duk wani kokari don a sasanta tsakanisu amma abun ya ci tura har said a Allah ya hada shi da Maryam, inda suka fara soyayya.

Bayan yan watanni sai kuma ya hadu da Jamila inda suka shiga soyayya, kuma yana son aurensu su duk biyun.

Sai ya sanar da Jamila cewa suna soyayya da Maryam inda ta amince da hakan. Amma matsalar shine ta yanda zai billowa Maryam kuma yana so ta kasance matarsa ta farko.

Ya bayyana cewa da kyar ya samu karfin gwiwar fada mata amma sai Maryam bata yi na’am d hakan ba, sai ya fara tausarta, yana zuwa wajenta akai-akai da bata kulawa na musamman da kuma yi mata siyayya.

KU KARANTA KUMA: Da zafi-zafi: Buhari, gwamnoni da shugabannin tsaro na cikin ganawar sirri

Ya fada mata cewa idan har tana son shi toh ya kamata ta damu da farin cikin shi , sannan idan auranta tare da Jamla ne farincikinsa toh sai ta amince, sai kawai ta mara mai baya.

Sai dai bai fada masu cewa tare zai aure su a tare ba. Sai dai ya samu iyayen Jamila ya fada masu halin da ake ciki na son hada auren amma basu nuna adawa da hakan ba.

Amma iyayen Maryam sai da aka kusa auren ya sanar masu, sai dai suka ce tunda yarsu ta san da batun toh basu da ja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel