Yawan mutanen da suka mutu a hare-haren yan bindiga a Niger ya tashi zuwa 47

Yawan mutanen da suka mutu a hare-haren yan bindiga a Niger ya tashi zuwa 47

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Niger (NSEEMA) a jiya Laraba, 12 ga watan Yuni ta bayyana adadin wadanda suka mutu a hare-haren da yan bindiga suja kai kan garuruwan Kwaki, Ajatayi, Gwassa, Barden Dawaki, Gyammamiya da Alewa duk a karamar ukumar Shirororo da ke jihar a matsayin 47.

Da farko an rahoto cewa a kashe mutum goma sha biyu a harin, amma Shugaban NSEMA, Malam Salihu Garba ya fada ma majiyarmu ta Daily Trust cewa an gano gawawwaki 47 zuwa iya Laraba.

Garba yace: “A yanzu da muke Magana, an gano gawawwaki 47 an kuma binne su. Daga cikinsu, 19 sun kasance daga Kwaki, ciki harda Sarkin Pawa wanda aka harba inda ya mutu daga bisani."

Yace Kwaki na iysa samun mafi yawan mutane da aka kashe saboda shine gari na farko da aka kai wa hari.

Yace daga cikin mutane 2,000 da suka zama marasa galihu, an sama wa 500 wajen zama a wani sansani na wucin gadi wanda hukumar ta kafa a Erena; yayinda sauran ke a Galadima-Kogo, Zubba, Kodobi da sauran garuruwa.

KU KARANTA KUMA: Nan ba da dadewa ba, Buhari da Tinubu za su gane El-Rufa'i munafiki ne - Shehu Sani

Ya kuma bayyana cewa wadanda aka jiwa rauni na karban magani a asibitoci a Erena da Kuta, yayinda wadanda ke da munanan rauni aka mika su ga manyan hukumomi lafiya a wajen yakin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel