Akwai rainin hankali a lamarin garkuwa da mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna – Shehu Aljan

Akwai rainin hankali a lamarin garkuwa da mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna – Shehu Aljan

Shahararren jami’in tsaron na sa-kai Alhaji Shehu Musa wanda aka fi sani da Aljan yayi tsokaci akan matsalar garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro da ya addabi yankin arewacin kasar.

Aljan wanda ya kware wajen kama barayin shanu, masu fashi da makami, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata miyagun ayyuka ya bayyana bakin zaren yadda za a iya kawo karshen lamarin.

A wata hira da jaridar Aminiya tayi da Aljan, tayi masa wasu tambayoyi ida shi kuma ya dunga bayar da amsoshinsu dalla-dalla.

Da aka tambaye shi kan me yake ganin ya kawo matsalar tsaro ta ki cinyewa a arewacin kasar Aljan yace: “Ka ga akwai wasu mutanen da ake kira ’Yan Caji Da Beli, wato wadanda suna nan zaune ba su da wata sana’a sai dai idan sun ji an yi ram da ’yan fashi ko masu garkuwa da mutane su je su samu kungiyoyinsu su karbi makudan kudade sannan su je su shiga su fita a tsakanin ’yan sanda da alkalai su ba su na goro su yi belin masu laifin, domin suna da lauyoyinsu.

"In dai ana son kawo karshen matsalar tsaro a Arewa to kuwa sai an yi maganinsu. Idan ba haka ba aikin banza ne ake yi, domin na sha kama barayi bayan ’yan kwanaki sai in ji an sake su kuma ka san komawa za su yi su ci gaba da sata, tun da sun san ko ma me suka yi sakinsu za a yi.”

Aljan yace akwai rainin hankali a garkuwa da ake yi da mutane a hanayr Abuja zuwa Kaduna. Domin a cewarsa idan mutum ya baro Kaduna zuwa Abuja da rana zai ga tarin motoci na yan sanda sama da guda 30 amma kuma sai dare yayi ace an tare hanya ana harbin mutane tare da janye su zuwa jeji, inda daga bisani za a nemi kudin fansa.

Ya kara da cewa: “Akwai damuwa fa. Ta ya ya za a ce masu kama mutanen nan har suna amfani da waya su kira ’yan uwan wadanda suka kama kuma a ce wai ba a iya kama su ba?”

Aljan ya kara da cewa: “Su ma a jami’an tsaron aikin da aka ce ana yi kawai duk karya ake yi. In aka ce maka aikin za a yi ai za a yi. Sannan kuma mafi yawa matsalar na nan a kauyukan da suke a kan hanyar.

"Mafi yawan mutane nan da suke a wadannan kauyuka ‘yan leken asiri ne na barayi. Sun san lokacin da ’yan sanda suke gama aikin rana da kuma lokacin da wasu za su karba su fara aikin dare. Don haka take sai su sanar da masu garkuwa da mutane.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa 12 ga watan Yuni yafi 29 ga watan Mayu muhimmanci - Babban jigon APC na kasa

Da aka tambaye shi kan mafita ga wannan matsala, Aljan yace: “Kasan maganin wannan hanyar ta Kaduna irinmu, ba wai sun ce su bindiga ba ta kama su ba? To ai Ayar Allah na kama su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel