Gwamna Tambuwal yayi sabbin nadi masu muhimmanci a gwamnatinsa

Gwamna Tambuwal yayi sabbin nadi masu muhimmanci a gwamnatinsa

- Gwamn Aminu Waziri tambuwal ya nada Ubandoman Sokoto, Hon. Saidu Umar a matsayin babban Sakataren gwamnatin jihar

- Tambuwal ya kuma amince da nadin Alhaji Mukhtar Umar Magori a matsayin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar

- Ya bukaci da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na yiwa mutane aiki

Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Aminu Waziri tambuwal ya nada Ubandoman Sokoto, Hon. Saidu Umar a matsayin babban Sakataren gwamnatin jihar.

Umar ya kasance tsohon kawmishinan kudi na jihar.

Hakan na kunshe ne a wani jawabi da Babban Darektan Tambuwal akan kafofin yada labarai da harkokin al’umma, Abubakar Shekara ya gabatar.

Gwamnan har ila yau ya amince da nadin Alhaji Mukhtar Umar Magori a matsayin shugaban ma’aikatan Gidan Gwamnatin Sokoto.

Tambuwa wanda ya taya jami’an biyu murna, ya bukaci da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na yiwa mutane aiki.

KU KARATA KUMA: Gwamnan Zamfara ya dakatar da Sarki da Hakimi

Gwamnan ya kuma roki Allah da ya jagorance su a sabon ayyukan da aka daura musu.

A wani labari a daban, Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnatin jihar Kwara ta karyata zancen dake yawo cewa ta sallami ma’aikatanta inda tace ko kadan wannan batun ba gaskiya bane.

A wani zance da ya fito daga hannun hadimin gwamna Abdulrahman Abdulrazak mai kula da sashen labarai, Agboola Olarewaju ya ce, “ Karyane gwamnatin Abdulrahman Abdulrazak bata kori ma’aikaci ko guda ba daga aiki.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel