Yadda Tinubu Ya Samar wa Matasa 500,000 Aiki a Ɓangare 1 Kacal
- Gwamnatin Tinubu ta samar da gidaje sama da 26,000 tare da samar da dubban ayyukan yi a sassa daban-daban na Najeriya
- APC ta ce asusun tallafin gidaje na Naira tiriliyan daya ya bayar da sama da Naira biliyan 158 ga masu sayen gidaje 2,269
- Shirin Renewed Hope Housing na Tinubu na gina dubban gidaje a Abuja, Kano da Legas da sauran garuruwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa ta jam’iyyar APC ta bayyana yadda Bola Tinubu ya samar da ayyukan yi.
Kwamitin ya ce ayyukan samar da gidaje da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar sun samar da gidaje sama da 26,000 tare da samar da ayyukan yi 525,100 a fadin Najeriya cikin shekaru uku.

Source: Twitter
Mai magana da yawun majalisar kuma Ministan Ma’adanai, Dele Alake, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamban 2026, cewar Punch.
Manyan ayyuka da gwamnati ke yi
Ya ce ana gudanar da ayyukan ne ta hannun hukumomin gwamnatin Tinubu guda uku domin bunkasa samar da gidaje masu saukin kudi da kuma samar da ayyukan yi ga ‘yan Najeriya.
Majalisar ta bayyana cewa asusun zuba jari kan gidaje na Ma’aikatar Kudi (MOFI Real Estate Investment Fund), wanda darajarsa ta kai Naira tiriliyan daya, ya samar da sama da Naira biliyan 158 na tallafin rancen gidaje ga mutane 2,269 zuwa ranar 31 ga Oktoban 2026.
A cewar sanarwar:
“Cikin shekaru uku da suka gabata, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta taimaka wajen samar da kudade da gina gidaje sama da 26,000, tare da samar da ayyukan yi 525,100 a bangaren gine-ginen gidaje a fadin Najeriya.”
Ta kara da cewa gwamnatin ta bullo da shirin Renewed Hope Housing domin samar da gidaje ga ‘yan Najeriya tare da bunkasa ayyukan yi ta hanyar gine-gine da sauran ayyukan da suka shafi wannan fanni.

Source: Getty Images
Jihohin da ake gina sababbin gidaje
Majalisar yakin neman zaben APC ta ce Ma’aikatar Gidaje da Raya Birane ta Tarayya tana gina gidaje 10,328 karkashin shirye-shiryen Renewed Hope Cities and Estates, wadanda ke matakai daban-daban na kammalawa.
Hukumar Samar da Gidaje ta Tarayya (FHA) kuma tana aikin samar da gidaje 3,341, ciki har da guda 1,550 da aka ware wa jami’an tsaro a Jabi da ke Abuja, cewar Vanguard.
A cikin ayyukan akwai gidaje 2,744 a birnin Renewed Hope da ke Abuja, guda 2,000 a Kano da kuma 2,084 a Legas.
Tinubu ya sha alwashin ceto daliban Borno
A baya, an ji cewa Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen ceto ɗaliban da aka sace a jihar Borno.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin wani gangamin siyasar APC a Maiduguri, inda ya kuma yaba wa jami’an tsaro bisa sadaukarwar da suke yi.
Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya gode wa Tinubu kan ayyukan raya ƙasa da gwamnatin tarayya ta gudanar a jihar.
Asali: Legit.ng

