An yankewa wani saurayi hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan kama shi dumu-dumu da hannu wurin kashe budurwarshi

An yankewa wani saurayi hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan kama shi dumu-dumu da hannu wurin kashe budurwarshi

Justis A. Jauro na baar kotun Yobe ya yanke ma wani matashi mai suna Muhammed Adamu hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon kasha budurwarsa mai shekaru 24, Hauwa Muhammad.

Yan sanda ne suka gurfanar da Adamu a gaban kotun bayan ya kashe Hauwa a lokacin wani musayar kalamai da suka yi a ranar 29 ga watan Mayun 2018.

Da yake yanke hukunci kan shari’an a jiya Talata, 11 ga watan Yuni, Justis Jauro, ya ayyana cewa dan sandaa mai karan ya kafa hujja fiye da tsammani cewa mai laifin ne ya kashe matashiyar. Don haka kotu ta kama shi da laifin kisan kai a karkashin sashi na 221 na kundin doka.

“Kamar yadda sashi na 273 na kundin doka ya tanadar, idan aka yanke wa mutum hukuncin kisa, za a kashe shi ne ta hanyar rataya. Don haka na yanke maka Muhammed Adamu hukuncin kisa ta hanyar rataya. Allah ya gafarta maka” inji alkalin.

Da yake zantawa da manema labarai bayan hukuncin, lauyan wanda ake kara, Mista M. Dauda, ya bayyana cewa zai yi nazari akan hukunci sannan akwai yiwuwar zai daukaka kara.

Da yake martani ga hukuncin, mai laifin yace ya amshi hukuncin a matsayin kaddarar da Allah ya shirya masa.

KU KARANTA KUMA: Rashin imani: Shugaban makaranta ya yiwa dalibarsa ‘yar shekara 4 fyade

“Na dade ina addu’a ga Allah akan hukunci mafi kyau. Na yarda cewa wannan ne hukuncin Allah a kaina sannan ya yi imanin cewa wannan hukuncin ne zabin Allah. Na amshe shi da hannu bibbiyu,” inji shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel