Kalli uwargidar gwamnan jihar Gombe da ke sanya dogon hijabi har kasa

Kalli uwargidar gwamnan jihar Gombe da ke sanya dogon hijabi har kasa

Kamar yadda muka sani hijabi wani tufafe ne da mata ke amfani dashi wajen yane kansu da jikinsu. Hijabi kan karawa mace kima da zati a cikin al’umman Musulmi kasancewar Allah ne ya umurci mata da su sanya shi.

Sai dai kamar yadda yake a yanzu a tsakanin matan wannan zamani ba kasafai suke son sanya hijabi ba, musamman gani da duke kamar yana rage masu kyawu da adonsu.Musamman ma a tsakanin matan manya da wadanda ke ganin su sun isa.

Hakan ne yasa wani mai amfani da Twitter ya je shafinsa domin jinjina wa uwargidar wani gwamna wacce ke sanya hijabi zuwa ko ina.

A kullun za ka ga Uwargidar gwamnan jihar Gombe Hajiya Asma’u Inuwa Yahaya, mata ga Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, sanye da hijabi.

Kalli uwargidar gwamnan jihar Gombe da ke sanya dogon hijabi har kasa
Kalli uwargidar gwamnan jihar Gombe da ke sanya dogon hijabi har kasa
Asali: Twitter

Matashin mai amfani da shafin Twitter mai suna Haji Shehu ya wallafa hotunan matar gwamnan a shafinsa.

Kalli uwargidar gwamnan jihar Gombe da ke sanya dogon hijabi har kasa
Kalli uwargidar gwamnan jihar Gombe da ke sanya dogon hijabi har kasa
Asali: Twitter

Haji Shehu yayi ikirarin cewa ita kadai ce matar gwamna da ke sanya hijabi cikin dukkanin matan gwamnonin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisar dattawa: Sanatoci 61 sun lamuncewa Lawan – Kungiyar kamfen

Yace: “Ita kadai ce uwargidar gwamna wacce ke sanya hijabi. Mai girma Hajiya Asma’u Inuwa Yahaya, uwargidar gwamnan jihar Gombe. Nuna mani uwargidar gwamnanka da ke sa hijab."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel