Dan takaitaccen tarihin marigayi Janar Sani Abacha yayinda ya cika shekaru 21 rasuwa a yau

Dan takaitaccen tarihin marigayi Janar Sani Abacha yayinda ya cika shekaru 21 rasuwa a yau

A yau Asabar, 8 ga watan Yuni ne, tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, Janar Sani Abacha ya cika shekaru 21 da mutuwa.

An haifi Janar Sani Abacha ranar 20 ga watan Satumbar shekarar 1943 a cikin garin Kano.

Ya yi makarantar Firamari a makarantar City Senior Primary School, Kano, sannan ya garzaya Government College, Kano, 1957-1962, daga nan kuma ya tafi makarantar Kwalejin horas da sojoji ta Kaduna Najeriya, 1962-1963.

Sannan ya wuce kwalejin Horas da Sojoji ta Aldershot dake Ingila, 1963, Kwalejin horas da dakarun kasa ta Warminster, ta Birtaniya 1966, 1971 Kwalejin sojoji ta Jaji dake Kaduna Nijeriya, 1976, Kwalejin nazarin manufofi da tsara dabarun

mulki ta Kuru, Jos, 1981, ya yi kuma wasu kwasa-kwasai da suka shafi harkar tsaro a Canada, Amurka a shekarar 1982.

Tun daga juyin mulki na farko a Najeriya a shekarar 1966 janar Sani Abacha ke taka rawar gani sai wanda aka yi wa Shagari da na Babangida da kuma wanda yaiwa Cif Ernest Shenakon.

KU KARANTA KUMA: Za mu bi umurnin kotu akan Rochas Okorocha - INEC

Allah ya yiwa Janar Sani Abacha rasuwa ranar 8 ga watan Yuni shekarar 1998 yana da shekaru 54 da haihuwa sakamakon ciwon zuciya.

Ya rasu ya bar mata daya Hajiya Maryam Abacha da 'ya 'ya tara mata uku da maza shida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel