Alhamdulillah: Al’umman Maiduguri sun yi bikin karamar sallah cikin kwanciyar hankali

Alhamdulillah: Al’umman Maiduguri sun yi bikin karamar sallah cikin kwanciyar hankali

Mazauna garin Maiduguri, babbar birnin jihar Maduguri a jiya, Talata, 4 ga watan Yuni sun yi bikin karamar Sallah cikin kwanciyar hankali da lumana, bayan yawan hare-hare da yan ta’addan Boko Haram suka kai kan garuruwa da dama a fadiun jihar Borno a yan makonnin da suka gabata.

Da misalin karfe 9:15 na safe, Babagana Zulum, wanda ya samu rakiyan Sanata Muhammadu Ali Ndume, Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Kanemi, Shehun Dikwa, Alhaji Muhammadu Masta II, da sauran manyan yan siyasa sun gudanar da sallah a masallacin idi na Ramat Square inda limamin idi, Muhammad Shettima Saleh, ya jagoranci Sallah.

Gwamna Zulum, wanda ya zanta da manema labarai bayan Sallah, ya taya al’umman Musulmi murna, inda yayi alkawarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar.

Ya bukaci mutanen jihar da su yi addu’an wanzuwar zaman lafiya domin a samu ci gaba a jihar.

KU KARANTA KUMA: Neman lafiya: Mazauna Abuja sun koma ga bokaye da masu maganin gargajiya

Anyi hawan daba a fadar Shehu, inda sarkin Borno da hakimansa suka birge tawagar gwamnan da dawakansu da aka yiwa ado da kayayyakin sarauta.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Jami’an tsaro na Civil Defence a Borno a ranar Laraba, 5 ga watan Yuni, sun tabbatar da kama wani Aliyu Muhammed, mai shekaru 24 wanda ake zargin shi kaiwa yan ta’addan Boko Haram kayayyakin hada bama-bamai a Maiduguri.

Kwamandan rundunar, Ibrahim Abdullahi ya bayyana hakan a hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Maiduguri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel