Gwamnatin Neja Ta Tabbatar da Kashe Mutum kusan 100 a Jihar
- Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya tabbatar da mutuwar mutum 74 sakamakon rikicin da ya ɓarke a Borgu
- Gwamnan ya sanar da cewa gwamnatin jihar za ta ba iyalan kowane mutum da ya mutu diyya ta Naira miliyan 2 don rage radadi
- Rundunar ’yan sanda ta kuma umarci tura ƙarin jami’an yaƙi da ta’addanci domin shawo kan matsalar tsaro a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Adadin mutanen da suka mutu a rikicin da ya ɓarke da aka kai farmaki matsugunin makiyayan Fulani a ƙaramar hukumar Borgu ta Jihar Neja ya kai 74.
Gwamnan jihar, Mohammed Umaru Bago, ne ya tabbatar da hakan yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai fadar Sarkin Borgu, Alhaji Halilu Sani Dantoro, a New Bussa, hedikwatar ƙaramar hukumar.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa rikicin ya biyo bayan wani hari da ’yan ta’adda suka kai a garin Lumman-Ba’are a ranar Asabar, inda suka kashe dagacin garin, Malam Bawa Muhammad, matarsa da ’ya’yansa uku, tare da ƙona fadarsa.
Yadda rikicin ya ɓarke a Borgu
Wani shugaban al’umma a Wawa ya shaida cewa ’yan banga daga Lumman-Ba’are sun ɗauki matakin ramuwar gayya bayan wani da suka kama da ake zargi da ta’addanci ya ce maharan sun fito ne daga garin Gada Oli.
Ya ce bayan samun wannan bayani, ’yan bangan sun taru da yawa suka nufi Gada Oli, suna zargin cewa za su kai farmaki domin kawar da ’yan ta’adda.
A cewarsa, sun riƙa harbin mutanen da suka haɗu da su a kan hanya, ciki har da waɗanda ke Wawa, inda suka kashe mutane da dama a wasu matsugunan Fulani.
A wani sako da ta wallafa a X, kungiyar Amnesty International ta yi zargin cewa wasu ne suka farmaki Fulani suka kashe sama da mutum 60 a cikinsu da ba su ji ba, ba su gani ba.
Alkawarin da Bago ya yi
Rahotanni sun nuna cewa Gwamna Bago ya yi kira ga ɓangarorin da ke rikicin da su ajiye makamansu su rungumi zaman lafiya.
Ya ce babu wanda ya yi nasara ko wanda aka kayar a rikicin, yana mai bayyana zaman tare da aka daɗe ana yi tsakanin al’ummar Kambari da Fulani.
Gwamnan ya sanar da cewa gwamnatin jihar za ta biya iyalan kowane mutum da ya mutu Naira miliyan 2, inda ya ce ana ci gaba da tantance waɗanda abin ya shafa.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati za ta tantance barnar da aka yi tare da sake gina al’ummomin da aka ƙona.
Bago ya ƙara da cewa za a shirya shirin afuwa domin ƙarfafa wa masu riƙe da makamai ba bisa ƙa’ida ba gwiwar miƙa su, tare da haɗin gwiwar Cibiyar Kula da Yaɗuwar Ƙananan Makamai.

Source: Original
A nasa ɓangaren, Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Olatunji Rilwan-Disu, ya bayar da umarnin tura ƙarin jami’an rundunar yaƙi da ta’addanci (CTU) zuwa yankin domin magance matsalar tsaro.
An kai wa Omo-Agege hari
A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, ya bayyana cewa harin da aka kai wa gangamin siyasarsa a Jihar Delta shi ne yunƙuri na biyar na kashe shi.
Omo-Agege ya zargi jami’an ’yan sanda da ke wajen taron da ƙin ɗaukar mataki a lokacin da wasu ’yan bindiga suka buɗe wa tawagarsa wuta.
A bayanin da ya yi bayan harin, ɗan takarar sanatan ya ce maharan sun jira sai ya miƙe domin fara jawabi kafin su fara harbe-harbe da nufin hallaka shi.
Asali: Legit.ng


