An kaddamar da Ahmed Wase a matsayin mataimakin kakakin majalisar wakilai

An kaddamar da Ahmed Wase a matsayin mataimakin kakakin majalisar wakilai

Ahmed Idris Wase ya zama mataimakin kakakin majalisar wakilai na tara bayan an gabatar dashi ba tare da abokin adawa ba.

An kaddamarda Ahmed Wase daga jihar Plateau a matsayin matamakin kakakin majalisar wakilai ne a yau, Talata, 11 ga watan Yuni yayin zaman majalisar a farko.

Wase ya bayyana ba tae da abokin adawa ba bayan Sada Soli daga jihar Katsina ya gabatar dashi a matsayin mai neman kujerar mataimakin kakakin majalisar.

A lokacin da magatakardar majalisa yayi sanarwa akan ko akwai wani da za a gabatar sai ya kaance babu kowa, don haka sai ya kaddamar da Idris a matsayin matamakin kakakin majalisar.

Dama shine dan takarar da jam’iyyar tafi so ya dare wannan kujerar.

A halin da ake ciki Legit.ng ta rahoto a baya cewa, Mataimakiyar shugaban jakadancin Amurka na Najeriya, Kathleen FitzGibbon, tayi kira ga sababbin shuwagabannin majalisa da su taimaka wajen magance matsalolin tsaro a Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Za mu kunyata masu cin hanci ta hanyar bayyana sunayensu - Buhari

FitzGibbon, daya daga cikin baki na musamman, wacce ta wakilci shugaban jakadancin, tayi kiran ne bayan da aka kaddamar da majalisar ta tara.

Ta kara da cewa, Majalisar tashiya yin aiki da wuri don a magance matsalolin tsaro, talauci da cigaban kasarnan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel