Tawagar APC Ta Yi Hadari a Hanyar Taron Tinubu, an Rasa Rayuka

Tawagar APC Ta Yi Hadari a Hanyar Taron Tinubu, an Rasa Rayuka

  • Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya yi jimamin rasuwar magoya bayan APC biyu da suka mutu a hatsarin mota a kan hanyar Biu zuwa Damaturu
  • Mutane 11 sun samu raunuka daban-daban a hatsarin yayin da suke tafiya Maiduguri domin halartar gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC
  • Gwamnan ya kuma ɗage gangamin APC na shiyyar Kudancin Borno da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar zuwa 2 ga Disamba, 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno – Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya miƙa saƙon ta’aziyya ga al’ummar Biu bayan rasuwar mutane biyu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a kan hanyar Biu zuwa Damaturu.

Mutanen na kan hanyarsu ta zuwa Maiduguri ne domin halartar gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, inda wasu mutane 11 suka samu raunuka daban-daban.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: An kashe mutane 5 suna cikin barci da tsakar dare a jihar Jigawa

Gwamna Babagana Zulum
Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum. Hoto: Dauda Iliya
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da mai ba gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Dauda Iliya, ya fitar a Facebook, Zulum ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga masarautar Biu da jihar Borno baki ɗaya.

Bayanin da Zulum ya yi

Gwamnan ya bayyana cewa ya samu labarin hatsarin da ya faru a kan hanyar Biu zuwa Damaturu da kuma wani mummunan lamari a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa cikin alhini.

Ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu, Ya ba su rahama, sannan Ya bai wa iyalansu haƙurin jure wannan babban rashi.

Jaridar Punch ta wallafa cewa gwamna Zuum ya roƙi Allah Ya ba mutane 11 da suka jikkata lafiya cikin gaggawa.

Zulum ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga al’ummar Damboa dangane da wani mummunan lamari da ya faru a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa, ba tare da bayyana ƙarin bayani kan abin da ya faru ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Neja ta tabbatar da kashe mutum kusan 100 a jihar

Taswirar jihar Borno
Taswirar jihar Borno a Najeriya.
Source: Original

An ɗage gangamin APC a Borno

Bayan faruwar waɗannan al’amura biyu, gwamnan ya bayar da umarnin ɗage gangamin yaƙin neman zaɓen APC na shiyyar Kudancin Borno da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar, 28 ga Nuwamba.

Mai magana da yawun gwamnan, Dauda Iliya, ya bayyana cewa an sauya ranar gudanar da gangamin zuwa Laraba, 2 ga Disamba, 2026.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya ziyarci Maiduguri a ranar Laraba domin halartar gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa.

'Yan APC sun rasu a Zamfara

A wani labarin, kun ji cewa shugabancin jam’iyyar APC na ƙasa ya yi jimamin rasuwar mambobinta 15 da suka mutu a wani hatsarin mota a Jihar Zamfara.

Jam’iyyar ta kuma miƙa ta’aziyya ga Gwamna Dauda Lawal, iyalan mamatan, gwamnatin jihar da sauran mambobinta, yayin da gwamnati ta dakatar da ayyukan yaƙin neman zaɓe da aka shirya a ƙaramar hukumar Maru.

Mutanen na kan hanyarsu daga ƙaramar hukumar Gummi zuwa Talata Mafara ne domin halartar gangamin APC, lokacin da hatsarin ya rutsa da su da misalin ƙarfe 12:30 na rana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng