Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Babban bankin Najeriya (CBN) a ranar Alhamis, 20 ga watan Fabrairu, ya ce zuwa yanzu ya dawo da sama da naira biliyan 60 daga bankuna a matsayin chajin da ake yiwa kwastamomi wanda ya wuce haddi.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bukaci kasar Amurka da ta soke hanin da ta yi mata na bai wa al’umman kasar bizar shiga kasarta. Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Aregbesola ne ya gabatar da wannan rokon.
Rahotanni sun kawo cewa an kwantar da wani likita, Cherechi Okonko a sashin bayar da agajin gaggawa na cibiyar lafiya ta tarayya, Owerri, jahar Imo, kan raunukan da matarsa ta ji masa.
Rahotanni sun kawo cewa wasu yan bindiga da ba a sani ba sun yi garkuwa da jami’an hukumar NSCDC a ranar Alhamis, 20 ga watan Fabrairu a yankin Ajegwu, karamar hukumar Ofu.
Tsohon sarkin Gwandu, Manjo Janar Mustapha Jokolo mai ritaya, ya nuna bakin ciki kan rikicin fadar shugaban kasa tsakanin mai ba shugaban kasa shawara a harkar tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno da shugaban ma’aikata Abba Kyari.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai yi murabus saboda rashin tsaro ba, cewa ana kokarin ganin an magance lamarin cikin nasara.
Rahotani sun kawo cewa babbar kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umurnin cewa a bai wa tsohon mai ba Shugaban kasa shawara a harkar tsaro a mulkin Jonathan, Sambo Dasuki fasfo din sa na fita kasashen waje.
Fitaccen jarumin nan na masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Sadiq Sani Sadiq wanda aka fi sani da dan marayan zaki, ya bayyana cewa sam bashi da ubangida a masana’antar.
Rundunar yan sandan Najeriya reshen jahar Nasarawa, ta tabbatar da kamun wata mata mai suna Paulina Santos, kan zargin yunkurin yin garkuwa da mahaifiyar kawarta.
Aisha Musa
Samu kari