Majalisar Dinkin Duniya Ta Sa Baki kan Harin Sojojin Sama da Ya Kashe Farar Hula a Zamfara
- Ana ci gaba da magana kan harin sojojin sama da ake zargin ya jawo asarar rayukan farar hula da dama a jihar Zamfara
- Majalisar dinkin duniya ta yi tsokaci kan harin tare da wani makamancinsa da sojojin Chadi suka kai a Tafkin Chadi
- Babban jami'in kare hakkin dan Adam na Majalisar dinkin duniya ya bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa cikin gaggawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Babban jami’in kare haƙƙin ɗan Adam na Majalisar dinkin duniya, Volker Turk, ya yi magana kan hare-haren da sojojin sama suka kai a Najeriya da Chadi.
Volker Turk ya buƙaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan rahotannin da ke cewa hare-haren sama daban-daban da dakarun Najeriya da na Chadi suka kai a Arewacin Najeriya sun kashe farar hula fiye da 100.

Kara karanta wannan
"Babu hujja," Sojojin Najeriya sun yi magana kan zargin kashe fiye da mutane 100 a Zamfara

Source: Twitter
Volker Turk ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin X a ranar Laraba, 13 ga watan Mayun 2026.
Ana fargabar kashe fararen hula a Zamfara
A cewar ƙungiyar Amnesty International an kashe akalla mutane 100 a harin da sojojin suka kai a kasuwar Tumfa da ke jihar Zamfara.
Yayin da take ambato shaidun gani da ido, Amnesty ta ce da dama daga cikin waɗanda aka kashe mata ne da kananan yara, sannan ta buƙaci hukumomi da su yi bincike kan harin.
Rahotanni sun bayyana cewa luguden wutar sojojin Chadi ya kashe masuntan Najeriya da dama da ke aiki a tsibiran da ke ƙarƙashin ikon Boko Haram, inda ake tilasta wa farar hula biyan haraji ga ƙungiyar 'yan ta'addan.
Me majalisar dinkin duniya ta ce kan harin?
“Na firgita da rahotannin cewa hare-haren saman da sojojin Najeriya suka kai a wata kasuwa a jihar Zamfara sun kashe aƙalla farar hula 100 ranar 10 ga Mayu tare da jikkata wasu da dama."
- Volker Turk
Ya ce ya kuma kasance “cikin fargaba da baƙin ciki” sakamakon rahotannin yawan asarar rayukan farar hula a hare-haren da jiragen yaƙin kasar Chadi suka kai tun ranar Juma’a a sansanonin Boko Haram da ke kan wasu tsibiran daji a yankin tafkin Chadi.
"Yana da matuƙar muhimmanci hukumomin Najeriya da na Chadi su gudanar da bincike cikin gaggawa, dalla-dalla, mai zaman kansa kuma ba tare da nuna son kai ba kan waɗannan abubuwa masu tada hankali."
- Volker Turk

Source: Twitter
Majalisar dinkin duniya ta bukaci a yi bincike
Ya ƙara da cewa dole ne dakarun sojojin biyu su dauki duk wani matakin kariya da za a iya don kauce wa cutar da farar hula.
“Dole ne a gudanar da ayyukansu na soja, ciki har da yaƙi da Boko Haram da abin da ake kira ‘Islamic State West Africa Province’ (ISWAP) cikin cikakken bin dokokin jin ƙai na ƙasa da ƙasa da kuma dokokin haƙƙin ɗan adam na ƙasa da ƙasa."
"Kada farar hula da ababen amfanin farar hula su taɓa zama abubuwan kai hari."
- Volker Turk
Gwamnatin Zamfara ta magantu kan harin sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnatin jihar Zamfara ta yi martani kan harin da sojojin sama suka kai a wata kasuwa a jihar.
Gwamnatin jihar Zamfara ta ce yankin da aka kai harin sanannen maboyar ‘yan bindiga ne da jami’an tsaro ke bibiyarsu.
Mai ba gwamnan Zamfara shawara kan harkokin tsaro, Ahmed Danmanga, ya ce gwamnatin jihar ba ta san akwai kasuwa a yankin ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

