Gwamnatin Najeriya ta nemi Amurka ta janye hanin ba da biza

Gwamnatin Najeriya ta nemi Amurka ta janye hanin ba da biza

- Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bukaci kasar Amurka da ta soke hanin da ta yi mata na bai wa al’umman kasar bizar shiga cikinta

- Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Aregbesola ne ya gabatar da wannan rokon

- A ranar Juma'a ne hanin zai fara aiki kan wasu kasashe

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bukaci kasar Amurka da ta soke hanin da ta yi mata na bai wa al’umman kasar bizar shiga kasarta.

Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Aregbesola ne ya gabatar da wannan rokon.

Gwamnatin Najeriya ta nemi Amurka ta janye hanin ba da biza
Gwamnatin Najeriya ta nemi Amurka ta janye hanin ba da biza
Asali: Depositphotos

Ministan ya yi rokon ne lokacin da jakadan Amurka a Najeriya ya ziyarce sa ranar Laraba kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

A ranar Juma'a ne hanin zai fara aiki kan 'yan kasashen Najeriya, Myanmar, Eritrea, Kyrgyzstan, Sudan da kuma Tanzania.

Jama'ar kasashen ba za su samu bizar Amurka ba da za ta iya ba su damar samun takardar izinin zama a kasar na din-din-din.

KU KARANTA KUMA: Tashin hankali: Mata ta yankewa mijinta harshe, hanci ta kuma kira mahaifiyarshi ta zo ta dauki gawarshi

A baya mun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump na kan yin wani yunkuri na kara yawan kasashen da Amurka za ta hana ‘yan kasar shiga cikinta.

Kasashen dai wadanda suka kasance guda hudu duk daga yankin Afirka sun hada da; Najeriya, Tanzania, Sudan da Eritrea.

Trump wanda ya bayyana hakan a wata hira da mujallar Wall Streer Journal a lokacin taron koli kan tattalin arziki na duniya a Davos, Switzerland, ya tabbatar da cewa yana kokarin fadada jerin sunayen kasashen da za a hana shiga Amurka amma bai fadi sunayensu ba.

Har ila yau a wani labarin kuma mun ji cewa Zhou Pingjian, jakadan kasar China a Najeriya, ya ce ofishin jakadancin kasar ta dakatar da ba yan Najeriya biza.

Hakan, a cewarsa yana daga cikin kokarin da ake na magance cutar coronavirus da ya billo a kasar Asiya, jaridar The Nation ta ruwaito.

Jaridar Legit.ng ta rahoto cewa sama da mutane dari uku ne suka mutu a kan mummunar annobar a China, yayinda kungiyar lafiya ta duniya ta kaddamar da shi a matsayin matsalar duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel