An tsaurara matakan tsaro a filin jirgin sama na Oshiomhole kan zuwan Oshiomhole

An tsaurara matakan tsaro a filin jirgin sama na Oshiomhole kan zuwan Oshiomhole

- An tsaurara matakan tsaro a filin jirgin sama na Benin

- An tsaurara tsaro ne a wajen domin dakile duk wani yunkuri na ci wa Oshiomhole zarafi ko kuma hana shi barin filin jirgin

- Hakan ya biyo bayan kokawar da wasu jiga-jigan APC suka yi kan harin da ake yunkurin kai wa Oshiomhole da mukarrabansa a Abuja

- An kuma gano gugun wasu matasa jibge a filin jirgin inda suke wakokin kin jinin Oshiomhole

Rahotanni sun kawo cewa an tsaurara matakan tsaro a filin jirgin sama na Benin kan tsoron yiwuwar kunyata Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Kwamrad Adams Oshiomhole.

A mashigin filin jirgin saman, akwai sojoji da motocin yan sanda biyu yayinda sauran jami’an rundunar tsaro ta DSS da NSCDC suka kasance a zube a wurare daban-daban na filin jirgin.

An kuma gano motan silken a tsaro ajiye a wajen ajiye motoci na filin jirgin saman.

An tattaro cewa an tsaurara tsaro ne a wajen domin dakile duk wani yunkuri na ci wa Oshiomhole zarafi ko kuma hana shi barin filin jirgin, jaridar The Nation ta ruwaito.

An tsaurara matakan tsaro a filin jirgin sama na Oshiomhole kan zuwan Oshiomhole
An tsaurara matakan tsaro a filin jirgin sama na Oshiomhole kan zuwan Oshiomhole
Asali: UGC

Mun samu labarin cewa an gano Dr. Pius Odubu, Janar Charles Airhiavbere, Samson Osagie da sauran jiga-jigan APC masu biyayya ga Oshiomhole a filin jirgin domin tarbansa.

An kuma gano gugun wasu matasa jibge a filin jirgin. An jiyo matasan suna wakokin kin jinin Oshiomhole.

Wata majiyar tsaro ta ce wasu jiga-jigan APC sun koka kan harin da ake yunkurin kai wa Oshiomhole da mukarrabansa a Abuja.

KU KARANTA KUMA: Ladanin Masallacin Landan da aka kai wa hari da wuka yace ya yafe duniya da lahira

A watan Disamban shekarar da ya gabata, an kwantar da magoya bayan APC 15 da ke biyayya ga Gwamna Obaseki a asibiti bayan an bude masu wuta tare da sojoji da yan sanda da ke masu rakiya da kuma wasu manyan masu fada-aji ciki harda Oshiomhole a hanyarsu ta zuwa gangamin siyasa a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel