Yanzu Yanzu: Buhari ba zai yi murabus saboda rashin tsaro ba – Gwamnatin tarayya

Yanzu Yanzu: Buhari ba zai yi murabus saboda rashin tsaro ba – Gwamnatin tarayya

- Gwamnatin tarayyar ta bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai yi murabus saboda rashin tsaro ba

- Ta kuma kaddamar da cewa ba za ta ja baya ba daga shirinta na daidaita soshiyal mediya ba

- Lai Mohammed ya jadadda cewa an dawo da tashin jiragen kasa da kasa a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Lagas

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai yi murabus saboda rashin tsaro ba.

Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed ya kuma bayyana cewa gwamnati ba za ta ja baya ba daga shirinta na daidaita soshiyal mediya ba.

Sannan ya jadadda cewa an dawo da tashin jiragen kasa da kasa a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Lagas.

Yanzu Yanzu: Buhari ba zai yi murabus saboda rashin tsaro ba – Gwamnatin tarayya
Yanzu Yanzu: Buhari ba zai yi murabus saboda rashin tsaro ba – Gwamnatin tarayya
Asali: Facebook

Muhammed ya bayyana hakan ne a wani taro a Abuja.

Ya ce: “Kamar yadda na fada a baya, kasar na fuskantar matsalolin tsaro, sannan ana magance matsalolin.

“Sai dai akwai wasu kiraye-kiraye a baya-bayan nan ciki harda masu neman Shugaban kasa ya yi murabus, ko ya tsige shugabannin tsaro.

“Ina so na sanar da cewar, gwamnati wacce ke ci gaba da samar da kayayyaki ga sojoji da hukumomin tsaro ta yarda da kokarinsu wajen magance rashin tsaro.

“Za a magance wadannan matsaloli cikin nasara. Sai dai zan shawarci dukkanin masu sharhi, musamman shugabannin siyasa da na addini da su yi taka-tsantsan a wannan lokaci da ake ciki.

KU KARANTA KUMA: Kotun Abuja ta yi umurnin ba Dasuki fasfo din sa na fita waje

“Ga wadanda ke kira ga Shugaban kasa da ya yi murabus, Ina fatan sanar da cewa: Shugaban kasa ba zai yi murabus ba.

“Yana da goyon bayan yan Najeriya na ya jagoranci al’amuran kasar har zuwa lokacin da wa’adin mulkinsa zai kare a watan Mayun 2023.”

A wani labarin kuma mun ji cew majalisar Dattawar Najeriya a ranar Alhamis ta gabatar da wani kudirin kafa hukuma ta musamman da za ta rika sauya wa tubabbun 'yan Boko Haram mummunan tunaninsu da koyar da su sana'o'i kafin daga baya a sake su su koma cikin al'umma.

Sanata Ibrahim Gaidam mai wakiltar Yobe ta Gabas ne ya gabatar da kudirin a gaban majalisa kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel