Cin amana: An kama wata mata da ta yi yunkurin garkuwa da mahaifiyar aminiyarta
- Rundunar yan sadan jahar Nasarawa, ta tabbatar da kamun wata mata mai suna Paulina Santos, kan zargin yunkurin yin garkuwa da mahaifiyar kawarta
- Kwamishinan yan sandan jahar, Mista Bola Longe ya bayyana cewa Paulina ta yi wani shiri don garkuwa da mahaifiyar aminiyarta wacce mijinta ke aiki a kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC)
- Ta yi hakan ne domin samun kudi daga wajensu a matsayin kudin fansar mahaifiyar aminiyar tata
- Longe ya ce za a gurfanar da ita a gaban kotu da zaran an kammala bincike
Rundunar yan sandan Najeriya reshen jahar Nasarawa, ta tabbatar da kamun wata mata mai suna Paulina Santos, kan zargin yunkurin yin garkuwa da mahaifiyar kawarta.
Da ake gurfanar da mai laifin tare das aura masu laifi a ranar Laraba, 19 ga watan Fabrairu a Lafia, babbar birnin jahar, kwamishinan yan sandan jahar, Mista Bola Longe ya yi zargin cewa Paulina ta yi wani shiri don garkuwa da mahaifiyar aminiyarta wacce mijinta ke aiki a kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC).
A cewarsa, “A ranar 11 ga watan Fabrairu, bisa ga bayanan kwararru, jami’a yan sanda da ke yaki da sashin masu garkuwa da mutane sun kama wata mata mai suna Paulina Santos wacce ta shirya garkuwa da mahaifiyar aminiyarta.”

Asali: Twitter
Mista Longe ya ce mai laifin ta fito ne daga karamar hukumar Ogbadigbo da ke jahar Benue, inda ya kara da cewa tana zama ne a Azuba Bashayi, yankin Lafia ta arewa, amma tana aiki a wani cibiyar lafiya.
Shugaban yan sandan ya yi bayanin cewa mai laifin ta tuntubi wani mutum da ya taimaka mata waen shirya yan ta’addan da za su aiwatar da aikin sace matar,kan cewa mijin kawarta da yaranta na aiki a NNPC, tare da kudirin samun makudan kudade daga wajensu a matsayin kudin fansa.
KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya sun ce ana biyanku da yawa - Buhari ga yan majalisa
Ya bayyana cewa mai laifin ta amshi bakin aikata hakan cewa za a gurfanar da ita a kotu da zaran an kammala bincike.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng