Ba ni da uban-gida a masana’antar Kannywood – Sadiq Sani Sadiq

Ba ni da uban-gida a masana’antar Kannywood – Sadiq Sani Sadiq

- Jarumi Sadiq Sani Sadiq wanda aka fi sani da dan marayan zaki, ya bayyana cewa sam bashi da ubangida a masana’antar Kannywood

- Sai dai Sadiq ya ce yana ganin mutuncin, Bello BMB, Ali Nuhu, Aminu Saira da Adam Zango

- Ya ce ya fi aminta da Rahama Sadau a gaba daya masana'antar

Fitaccen jarumin nan na masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Sadiq Sani Sadiq wanda aka fi sani da dan marayan zaki, ya bayyana cewa sam bashi da ubangida a masana’antar.

A hira da ya yi da sashin BBC Hausa, Sadiq ya bayyana cewa babu wanda ya koya masa sana’ar fim, cewa da kansa ya kai kansa.

Sai dai jarumin ya bayyana cewa akwai wasu mutane da yake ganin kimarsu matuka a masana’antar saboda wasu dalilai amma ba wai ubanningidansa bane.

Ba ni da uban-gida a masana’antar Kannywood – Sadiq Sani Sadiq
Ba ni da uban-gida a masana’antar Kannywood – Sadiq Sani Sadiq
Asali: Twitter

Ya lissafa wadannan mutane a matsayin Bello Muhammad Bello wanda aka fi sani da BMB, inda ya ce shine silar zuwansa masana’antar, sai Ali Nuhu wanda a cewarsa ya zauna a gidansa a lokacin da ya zo garin Kano, sai Aminu Saira wanda ya ce ya sanya sa a manyan fina-finai a lokacin da duniya bata yarda zai iya taka rawar gani ba ciki harda fim din dan marayan zaki, sannan daga karshe ya ambaci Adam A. Zango wanda a cewarsa ya zauna karkashin kamfaninsa.

Da aka tambaye sa kan ko wacece budurwarsa a Kannywood, sai ya ce "Ba ni da budurwa a Kannywood yanzu".

KU KARANTA KUMA: Cin amana: An kama wata mata da ta yi yunkurin garkuwa da mahaifiyar aminiyarta

Da aka tambaye shi wanene amininsa a masana’antyar, Sadiq ya ce Rahama Sadau ce aminiyarsa, domin a cewarsa ya fi yarda da ita sama da kowa don ya san za ta boye masa sirrinsa kamar yadda shima zai boye mata nata.

Sannan daga karshe jarumin ya jadadda soyayyarsa ga matarsa, inda ya ce yana mata irin so da baki ba zai furta ba sai zuciya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel