CBN ya mayar da sama a biliyan 60 da bankuna suka chaji kwastamomi wanda ya wuce haddi

CBN ya mayar da sama a biliyan 60 da bankuna suka chaji kwastamomi wanda ya wuce haddi

- Babban bankin Najeriya (CBN) ya ce zuwa yanzu ya dawo da sama da naira biliyan 60 daga bankuna a matsayin chajin da ake yiwa kwastamomi wanda ya wuce haddi

- Bankin ya kuma ce ya mayar wa da kwastamomin da abun ya shafa kudadensu

- An dawo da kudaden ne biyo bayan korafin da kwastamomi 13,000 suka yi kan yawan chajin da bankuna ke yiwa asusun su wanda baya bisa ka’ida

Babban bankin Najeriya (CBN) a ranar Alhamis, 20 ga watan Fabrairu, ya ce zuwa yanzu ya dawo da sama da naira biliyan 60 daga bankuna a matsayin chajin da ake yiwa kwastamomi wanda ya wuce haddi.

Bankin ya kuma ce ya mayar wa da kwastamomin da abun ya shafa kudadensu.

Hakan na zuwa ne yayinda bankin ya sanar da cewa ya fara shirye-shiryen samar da ayyuka miliyan 10 a shekaru biyar masu zuwa ta hanyar zuba jari a noma, ya hanyar amfani da sumfurin kayayyaki 10.

CBN ya mayar da sama a biliyan 60 da bankuna suka chaji kwastamomi wanda ya wuce haddi
CBN ya mayar da sama a biliyan 60 da bankuna suka chaji kwastamomi wanda ya wuce haddi
Asali: UGC

Da yake magana a taron wayar da kan kwastamomi na kwanaki biyu a Owerri, babbar birnin jahar Imo, daraktan labarai na CBN, Mista Isaac Okorafor ya ce an gano chajin bankin da ake yiwa kwastamomin ne ta sashin kare hakkin kwastamomi na bankin.

A cewarsa, an dawo da kudaden ne biyo bayan korafin da kwastamomi 13,000 suka yi kan yawan chajin da bankuna ke yiwa asusun su wanda baya bisa ka’ida.

Okorafor wanda ya kuma bayyana cewa CBN ya hukunta bankunan da abun ya wakana daga wajen su, ya bayyana cewa babban bankin ya jajirce don ganin ba a damfari kwastamomi ta hanyar chajin da ya wuce haddi daga bankunansu.

Ya Kara da cewa CBN ya dauki mataki don lura da bankuna da kuma tabbatar da cewar ba a wofantar da ajiyar kwastamomi ba.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Najeriya ta nemi Amurka ta janye hanin ba da biza

Ya yi amfani da damar wajen shawartan kwastamomin banki da su kai karar duk wani lamari da suke zargin an yi masu chaji ba bisa doka ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel