Kotun Kaduna ta saki 'yan Shi'a 100

Kotun Kaduna ta saki 'yan Shi'a 100

Rahotanni sun kawo cewa wata babbar kotu a jahar Kaduna ta saki mambobin kungiyar yan uwa Musulmai na Shi’a.

A wata sanarwa daga kakakin kungiyar, Ibrahim Musa zuwa ga manema labarai a ranar Juma’a, 21 ga watan Fabrairu, ya bayyana cewa mambobin kungiyar da kotu ta saki su ne rukunin karshe da aka sake tun da aka kama su a 2015, shafin BBC ta ruwaito.

Ya ce: "Wannan ya kawo karshen shari'ar shekaru hudu da muke yi, inda gwamnatin jahar Kaduna ta yi karar mambobin kungiyar IMN kusan 200 bayan sojojin Najeriya sun kai musu hari a watan Disambar 2015, lamarin da ya kai da kisan fiye da mutum dubu da kuma binne su a wani katon kabari a asirce."

Kotun Kaduna ta saki 'yan Shi'a 100
Kotun Kaduna ta saki 'yan Shi'a 100
Asali: Twitter

Ya kara da cewa sakin da aka yi wa mabiya kungiyar ya wanke su da shugabanninsu daga dukkan zargin da ya kai ga kisan da soji suka yi wa takwarorinsu a Zaria.

KU KARANTA KUMA: Tashin hankali: Mata ta yankewa mijinta harshe, hanci ta kuma kira mahaifiyarshi ta zo ta dauki gawarshi

Har yanzu dai shugaban kungiyar, El-Zakzaky da uwargidarsa na tsare a hannun hukumomin tsaro, duk da umarnin sakinsu da kotuna daban-daban suka yi.

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Eyinnaya Abaribe, a ranar Talata ya yi kira ga fadar shugaban kasa ta karasa abinda ta fara ta sako Sheikh Ibrahmm El-Zakzaky da sauran wadanda ke halin da ya ke ciki kamar tsohon mai bayar da shawara kan tsaro, Sambo Dasuku da dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore.

Sanarwar da mai bashi shawara a kan fanin kafafen watsa labarai, Uchenna Awom ya fitar ta ce Abaribe ya yi wannan jawabin ne bayan sakin Dasuki da Sowore kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban na marasa rinjaye ya ce shima El-Zakzaky da sauran wadanda ake tsare da su duk kotu ta bayar da su beli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel