Kotun Abuja ta yi umurnin ba Dasuki fasfo din sa na fita waje

Kotun Abuja ta yi umurnin ba Dasuki fasfo din sa na fita waje

Rahotani sun kawo cewa babbar kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umurnin cewa a bai wa tsohon mai ba Shugaban kasa shawara a harkar tsaro a mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Sambo Dasuki fasfo din sa na fita kasashen waje.

Mai Shari’a Husaini Baba-Yusuf ya bayar da umarnin ne bayan lauyan Dasuki, Ahmed Raji ya rubuta takardar neman a bai wa wanda ya ke karewan fasfo din sa.

Raji ya gabatar wa kotu kwararan dalilan neman a bayar da fasfo din, inda ya rika jawo wasu ayoyi daga cikin Kundin Dokokin Najeriya na Sashe na1, na 2, na 491 da kuma na 492(3) na 2015.

Lauyan ya ce fasfo din Dasuki ya wuce wa’adi da adadin shekarun da za a yi amfani da shi. Don haka akwai bukatar gaggauta sabunta shi.

Alkali ya amince kasancewa shi ma mai gabatar da kara bai yi wata jayayya a kan bayar da fasfo din ko kada a bayar ba.

Daga nan sai Mai Shari’a ya umarci Magatakardar Kotu ya bada fasfo din domin a je a sabunta shi, saboda ya wuce wa’adin da gwamnati ta amince a yi amfani da shi.

Kotun Abuja ta yi umurnin ba Dasuki fasfo din sa na fita waje
Kotun Abuja ta yi umurnin ba Dasuki fasfo din sa na fita waje
Asali: Twitter

Daga nan sai aka daga sauraren karar zuwa ranar 13 ga watan Maris, 2020 domin ci gaba da sauraron shari’a.

KU KARANTA KUMA: Cin amana: An kama wata mata da ta yi yunkurin garkuwa da mahaifiyar aminiyarta

Ku nuna cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC ) ce ta gurfanar da Dasuki kotu, inda ake tuhumar sa da yin babakere a kan kudaden sayen makamai.

A cikin kara mai lamba FCT/HC/CR/42/2015, ana tuhumar sa ne tare da tsohon karamin ministan kudi, Bashir Yuguda, tsohon gwamnan Sokoto Attahiru Bafarawa da dan sa Sagir da kuma kamfanin Bafarawa mai suna Dalhatu Investment Limited.

Ana tuhumar su da laifuka 25, wadanda suka shafi kwashe tsabar kudi har naira bilyan 19.4.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel