Tsohon dogarin Buhari ya nemi a tsige Monguno, Kyari da shugabannin tsaro

Tsohon dogarin Buhari ya nemi a tsige Monguno, Kyari da shugabannin tsaro

Tsohon sarkin Gwandu, Manjo Janar Mustapha Jokolo mai ritaya, ya nuna bakin ciki kan rikicin fadar shugaban kasa tsakanin mai ba shugaban kasa shawara a harkar tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno da shugaban ma’aikata Abba Kyari.

Jakolo wanda ya kasance dogarin shugaban kasa Muhammadu Buhari a lokacin da ya ke shugabanci a mulkin soja, ya yi kira ga Shugaban kasar a kan ya tsige su.

Manjo Jakolo ya kuma bukaci shugaba Buhari da ya saurari muryoyin yan Najeriya sannan ya tsige shugabannin tsaro.

Basaraken wanda ya yi magana a wani shirin gidan radiyo a Kaduna ya bayyana cewa ba a taba samun sabani a tsakanin manyan jami’an gwamnati ba a lokacin mulkin soja saboda suna mutunta mukamin kowa da gudun shiga sharo ba shanu.

Ya ce, har sai dai idan shugaban kasa, Shugaban tsaro da shugaban ma’aikatan shugaban kasa sun bi tsarin al’umman Najeriya, idan ba haka ba sai Allah na kallonsu saboda Najeriya ta fi karfin kowani mutum.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ba zai yi murabus saboda rashin tsaro ba – Gwamnatin tarayya

Kan shugabannin tsaro, ya ce yan Najeriya basu ji dadin shugabannin tsaron ba sannan cewa kamata ya yi a tsige su sannan a sauya su da wasu da suka fi su.

A baya mun samu labari cewa an samu sabani tsakanin wasu Jiga-jigai a gwamnatin Buhari, inda NSA Babagana Monguno ya ke zargin Abba Kyari da yin ba-ba-kere a fadar shugaban kasa.

Janar Babagana Monguno mai ritaya ya na zargin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, da shiga tsakanin wasu Jami’an gwamnati da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jaridar Premium Times ce ta fitar da wannan rahoto na musamman a Ranar Litinin, 17 ga Watan Fubrairun 2020. Abin har ta kai Babagana Monguno ya nemi a daina sauraron Abba Kyari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng