Yanzu Yanzu: An yi garkuwa da jami’an NSCDC 4 a Kogi

Yanzu Yanzu: An yi garkuwa da jami’an NSCDC 4 a Kogi

- Wasu yan bindiga da ba a sani ba sun yi garkuwa da jami’an hukumar NSCDC a ranar Alhamis, 20 ga watan Fabrairu a yankin Ajegwu, karamar hukumar Ofu

- Jami’an na a hanyarsu na zuwa jahar Benue, domin halartan jarrabawar karin girma

- Kakakin yan sanda a jahar, Williams Ayah ya tabbatar da lamarin

Rahotanni sun kawo cewa wasu yan bindiga da ba a sani ba sun yi garkuwa da jami’an hukumar NSCDC a ranar Alhamis, 20 ga watan Fabrairu a yankin Ajegwu, karamar hukumar Ofu.

An tattaro cewa jami’an na a hanyarsu na zuwa jahar Benue, domin halartan jarrabawar karin girma.

Wata majiya ta kusa da daya daga cikin jami’an da aka sace ta bayyana cewa jami’ian na tafiya ne a motar aiki lokacin da aka yi garkuwa da su a mararrabar Ajegwu, hanyar Itobe-Anyigba.

Yanzu Yanzu: An yi garkuwa da jami’an NSCDC 4 a Kogi
Yanzu Yanzu: An yi garkuwa da jami’an NSCDC 4 a Kogi
Asali: UGC

Majiyar wacce ta nemi a sakaya sunanta ta kara da cewa mutum na biyar a cikinsu ya tsere yayinda aka tisa keyarsu zuwa cikin daji.

Ya kara da cewa tuni masu garkuwan suka kira iyalan mutanen inda suka nemi a bayar da kudin fansa naira miliyan 30 kafin su sake su.

Da aka tuntube shi, kwamandan rundunar a jahar, Mista Peter Samuel Maigari ya ce ba zai iya tabbatar da lamarin ba. Ya ce zai yi jawabi da zaran ya samu karin bayani kan lamarin.

KU KARANTA KUMA: Fyade: An yankewa malamin jami'a hukuncin shekaru 21 a gidan gyaran hali

Kakakin yan sanda a jahar, Williams Ayah ya tabbatar da lamarin.

Ayah ya bayyana cewa sama da mutane hudu ciki harda jami’an NSCDC aka sace, inda ya yi alkawarin yin karin bayani kan lamarin.

A wani labarin kuma, mun ji cewa rundunar ‘Yan Sandan jihar Katsina sun kashe fitinannen Mai garkuwa da mutanen nan watau Abubakar Nayabale, sannan kuma sun kama wani, Tanimu Salisu.

Jami’an tsaron sun kashe Abubakar Nayabale ne a karamar hukumar Kurfi. Kakakin ‘Yan Sandan jihar, SP Gambo Isah, ya bayyanawa ‘Yan jarida wannan dazu.

Gambo Isah ya bada wannan sanarwa ne a Ranar Alhamis, 20 ga Watan Junairu, 2020. Jawabin ya ce sun kashe Nayabale ne bayan ya kai hari a wani Kauye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel