Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta kira wani taron gaggawa na masu ruwa da tsaki, wanda za a gudanar a ranar Talata, 17 ga watan Maris, 2020 a Abuja.
Mataimakin babban sakataren jam’iyyar na kasa, Mista Agbo Emmanuel ne ya sanya hannu kan takardar da ke dauke da jerin sunayen wadanda abun ya shafa sannan ya manna shi a akwatin sanarwa na jam’iyyar wanda ke sakatariyar ta.
Rahotanni sun kawo cewa jami’an tsaro sun hana wasu hadiman Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole shiga sakatariyar jam’iyyar.
Wata babbar kotun Kano da ke zama a hanyar Miller ta yanke wa wani mutum mai suna Yakubu Dalha na kauyen Tsangaya a karamar hukumar Albasu hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Kwamishinan Lafiya a jahar Legas Farfesa Akin Abayomi ya tabbatar da killace wasu mutum uku da ake zargi sun kamu da cura Coronavirus. Kwamishinan na jahar Lagas ya bayyana cewa an yiwa marasa lafiyan gwaji sannan an killace su.
Gwamnan jahar Ekiti, Kayode Fayemi, ya ce ayyukansa ba yunkuri ne na karban mulki daga wajen Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba a 2023.
Ayyukan siyasa a sakatariyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki sun durkushe tun bayan da babban kotun birnin tarayya ta dakatar da Shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole.
Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa, Salihu Mustapha ya ce kotun daukaka kara ce kadai za ta iya dawo da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyyar.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Justis Monica B. Dongban Mensem a matsayin Mukaddashin Shugaban kotun daukaka kara na tsawon watanni uku.
Aisha Musa
Samu kari