Toh fah: Jam’iyyar PDP ta sallami kaso 50 na ma’aikata a sakatariyarta

Toh fah: Jam’iyyar PDP ta sallami kaso 50 na ma’aikata a sakatariyarta

- Babbar jam'iyyar adawa ta kasa wato PDP ta sallami kaso 50 cikin 100 na ma’aikatan sakatariyar ta

- Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mataimakin babban sakataren jam’iyyar na kasa, Mista Agbo Emmanuel

- Koda dai ba a bayyana dalilin salamar nasu ba a jikin sanarwar amma wani jami’in jam’iyyar da ya yi martani kan lamarin ya ce basu da kudi don haka ya zama dole su rage yawansu

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sallami kaso 50 cikin 100 na ma’aikatan sakatariyar ta.

Mataimakin babban sakataren jam’iyyar na kasa, Mista Agbo Emmanuel ne ya sanya hannu kan takardar da ke dauke da jerin sunayen wadanda abun ya shafa sannan ya manna shi a akwatin sanarwa na jam’iyyar wanda ke sakatariyar ta na Abuja a ranar Juma’a, 6 ga watan Maris.

Toh fah: Jam’iyyar PDP ta sallami kaso 50 na ma’aikata a sakatariyarta

Toh fah: Jam’iyyar PDP ta sallami kaso 50 na ma’aikata a sakatariyarta
Source: UGC

An kuma bukaci dukkanin ma’aikatan da lamarin ya shafa da su mika duk wasu kayayyakin aiki da ke a hannunsu sannan su tabbatar an tantance su domin biyansu duk wani bashi da suke bi.

Sai dai kuma ba a bayyana dalilin salamar nasu ba a jikin sanarwar amma Wani jami’in jam’iyyar da ya yi martani kan lamarin ya ce: “bamu da kudi don haka ya zama dole mu rage yawanmu.”

KU KARANTA KUMA: Jerin ayyuka 35 da Buhari zai yi da bashin $22.7bn da zai karbo

A wani labari na daban, mun ji cewa jami’an tsaro sun hana wasu hadiman Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole shiga sakatariyar jam’iyyar.

An hana ma’aikatan wadanda suka isa wajen cikin wata mota kirar Toyota Jeep baka shiga sakatariyar duk da cewar an gane ko wanene su. Jami’an tsaron sun bukace su da su bar wajen kofar shiga ofishin jam’iyyar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an gano ma’aikatan da ke adawa da Oshiomhole ma a tsaye suna kallon duk diramar da ke wakana a sakatariyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel