Dakatar da Oshiomhole: Ayyuka sun tsaya cak a sakatariyar APC na kasa

Dakatar da Oshiomhole: Ayyuka sun tsaya cak a sakatariyar APC na kasa

- Ayyuka sun tsaya cak a sakatariyar APC mai mulki sun durkushe tun bayan da babban kotun birnin tarayya ta dakatar da Shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole

- Ma'aikatan sakatariyar sun kaurace wa zuwa aiki bayan jami’an tsaro sun mamaye sakatariyar don tabbatar da ganin an bi umurnin hukuncin da kotun ta yanke

- Sai dai kuma babbar kotun tarayya da ke Kano a ranar Alhamis karkashin jagorancin Jastis Lewis Allagoa ta yi umurnin barin komai yadda yake a baya a game da lamarin dakatar da Oshiomhole

Ayyukan siyasa a sakatariyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki sun durkushe tun bayan da babban kotun birnin tarayya ta dakatar da Shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An tattaro cewa ma’aikata a ofishin ba su hallara don kama ayyukan gabansu ba har karfe 12:05 na ranar Alhamis, lamarin da ya afku bayan jami’an tsaro sun mamaye sakatariyar don tabbatar da ganin an bi umurnin hukuncin da kotun ta yanke.

Dakatar da Oshiomhole: Ayyuka sun tsaya cak a sakatariyar APC na kasa
Dakatar da Oshiomhole: Ayyuka sun tsaya cak a sakatariyar APC na kasa
Asali: Facebook

A halin da ake ciki, wata babbar kotun tarayya da ke Kano a ranar Alhamis, 6 ga watan Maris karkashin jagorancin Jastis Lewis Allagoa ta yi umurnin barin komai yadda yake a baya a game daa lamarin dakatar da Oshiomhole.

Sai dai da yake martani kan batun, mataimakin Shugaban jam’iyyar na kasa (arewa maso gabas) Mustapha Salihu a yayin hira da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar ta kasa, ya yi korafin cewa ba zai yiwu kotun daidaita tsakani guda biyu su zauna kan lamari guda ba.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun cika hannu da kansiloli 3 a jahar Zamfara, sun nemi naira miliyan 40

A baya mun ji cewa Shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Kwamared Adams Oshiomole ya bayyana dalilin da yasa wasu yayan jam’iyyar APC wadanda yake kallonsu a matsayin makiyansa suke kokarin tsige shi daga kujerar shugabancin jam’iyyar.

Daily Trust ta ruwaito Oshiomole ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru jim kadan bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnatin Najeriya a ranar Alhamis.

Wannan jawabi na Oshiomole ya zo ne jim kadan bayan wata babbar kotun tarayya dake zamanta a jahar Kano ta soke dakatarwar da wata babbar kotun babban birnin tarayya Abuja ta yi masa a ranar Laraba.

A cewarsa, ya kai ziyarar ne domin bayyana ma shugaban kasa halin da ake ciki a tirka tirkar da ta dabaibaye jam’iyyar APC, sa’annan yace akwai wani minista a gwamnatin Buhari da wasu gwamnoni dake shirya masa duk wani tuggu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng