Yan sanda sun kama masu asiri 3 da kan mutum a Lagas

Yan sanda sun kama masu asiri 3 da kan mutum a Lagas

Rundunar yan sandan Najeriya reshen jahar Lagas ta kama wasu mutane uku da ake zargi da cire kan wani mutum daga wani makabarta domin yin asiri dashi.

Wani jawabi daga Bala Elkana, kakakin yan sandan jahar Lagas a ranar Lahadi, ya ce yan sanda daga sashi na ‘E’ na Festac ne suka kama masu laifin.

Mista Elkana ya ambaci sunayensu a matsayin Dauda Tijani mai shekara 42; wanda ke zama a gida mai lamba 23 unguwar Omomwunm, Orege Ajegunle; Obalawale Shodolamu mai shekara 79, wanda ya kasance boka da kuma Seun Falaba mai shekara 37; wanda ya kasance ma’aikaci na makabartar Trinity a Ajegunle.

Yan sanda sun kama masu asiri 3 da kan mutum a Lagas
Yan sanda sun kama masu asiri 3 da kan mutum a Lagas
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa Yan sanda sun kama Mista Tijani a tashar mota na Alakija hanyar babbar titin Lagos-Badagry, bayan sun same shi da jakar Leda dauke da kan mutum.

“Mai laifin ya tona cewa bokan ne ya aike shi ya je ya karbo masa kan daga wajen ma’aikacin makabartar.

“Bokan ya yi ikirarin cewa ya siyi kan ne daga waje Falana kan naira 10,000.

“Bokan ya kan nika kan ne tare da wasu abubuwa wajen hada wa abokan harkarsa magunguna,” in ji Elkana.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa muka fasa tayar motar da aka dauko mai nakuda - FRSC

Ya bayyana cewa mutum na ukun ya tona cewa ya kan haka kaburbura sannan ya cire kawunan mutane yana siyarwa da bokaye.

Ya kuma bayyana cewa ana gudanar da bincike sannan za a tura masu laifin kotu da zaran an kammala.

A wani labari na daban, mun ji cewa Jami’an rundunar binciken manyan laifuka na rundunar Yansandan Najeriya,SCIID, sun kaddmar da bincike kan dalilin da ya sabbaba mutuwar wani mutumi dan shekara 49 mai suna Babatunde Ishola.

Ana zargin wata daliba yar shekara 16 mai suna Timilehin Taiwo, diyar abokinsa ne ta kashe shi a lokacin da ya yi kokarin haike mata da nufin yin lalata da ita ta hanyar fyade, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel