Coronavirus: Buhari ya shiga ganawar sirri da Gwamna Sanwo-Olu a fadar Villa

Coronavirus: Buhari ya shiga ganawar sirri da Gwamna Sanwo-Olu a fadar Villa

- Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ziyarci fadar Shugaban kasa a ranar Lahadi, 8 ga watan Maris

- Gwamnan ya yi ganawar sirri tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Ganawar ya ba Sanwo-Olu damar sanar da Shugaban kasar kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen hana yaduwar cutar coronavirus a Lagas

Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jahar Lagas ya yi ganawar sirri tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Villa, Abuja.

Manema labarai na fadar Shugaban kasa sun tabbatar da ganawar wanda ya gudana a ranar Lahadi, 8 ga watan Maris, jaridar The Nation ta ruwaito.

An tattaro cewa ganawar tsakanin gwamnan jahar Lagas da Shugaban kasar ya zo wa manema labaran fadar Shugaban kasa a bazata.

Channels TV ta ruwaito cewa Sanwo-Olu ya yi amfani da damar wajen sanarwa da Shugaban kasar kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen hana yaduwar cutar coronavirus a Lagas.

Coronavirus: Buhari ya shiga ganawar sirri da Gwamna Sanwo-Olu a fadar Villa
Coronavirus: Buhari ya shiga ganawar sirri da Gwamna Sanwo-Olu a fadar Villa
Asali: UGC

Coronavirus: Buhari ya shiga ganawar sirri da Gwamna Sanwo-Olu a fadar Villa
Coronavirus: Buhari ya shiga ganawar sirri da Gwamna Sanwo-Olu a fadar Villa
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Oshiomhole zai san makomarsa yayinda APC ta kira taron gaggawa a tsaka da rikicin cikin gidanta

A wani labari na daban, mun ji cewa alamu na nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya na kokarin ganin karshen rigimar da ake fama da ita a cikin tafiyar jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Rahotanni su na nuna mana cewa shugaban kasar ya fara sa baki a rikicin da APC ta samu kanta bayan kotu ta dakatar da Adams Oshiomhole daga shugaban jam’iyya.

Wata majiya daga Jaridar The Nation ta ce shugaba Buhari ya nada wasu mutum uku da su shiga su fita domin ganin an sasanta Oshiomhole da sauran ‘yan jam’iyyar.

Akwai yiwuwar kuma shugaban kasar ya roki shugabannin APC na kasa su bada gudumuwarsu wajen ganin an kashe wutar rigimar da ta barkewa APC mai mulki.

A cewar Majiyar, Buhari da na-kusa da shi ba su jin dadin yadda abubuwa su ke kankama a APC a daidai lokacin da ya ke kokarin jan ragamar shugabancin kasar.

Wannan rikicin cikin gida da ya aukowa APC zai iya karkatar da hankalin gwamnatin shugaba Buhari daga yin aikin da ke gabanta a yanzu, don haka ta fara daukar mataki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng