Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Majalisar dokokin jahar Kano za ta kara bincikar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi, kan wasu korafe-korafe da wasu mazauna jahar suka gabatar a gabanta, inda suke zargin sa da ci wa al’adun garin fuska.
Wata babbar kotun birnin tarayya a Jabi, Abuja ta dakatar da Adams Oshiomhole daga matsayin Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Folashade Yemi Esan a matsayin sabuwar Shugaban ma’aikatan tarayya a ranar Laraba, 4 ga watan Maris. An yi bikin rantsarwar Esan a zauren majalisar zartarwa na fadar shugaban kasa.
Rahotanni sun kawo cewa a yanzu haka Damboa, hedkwatar wata karamar hukuma a jahar Borno na karkashin harin yan ta’addan Boko Haram. Mazauna yankin sun ce yan ta’addan sun zo su da yawa da misalin karfe 6:30 na safiyar yau Laraba.
Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan rundunar soji, Sanata Ali Ndume, a jiya Talata ya koka kan rashin gaskiya da ake nunawa wajen daukar aiki a hukumomin gwamnatin tarayya, cewa ya zama dole a dauki hakan a matsayin laifi.
Shugaban hukumar hana yaduwar cutuka a Najeriya (NCDC), Chikwe Ihekweazu ya shiga sahun killace kansa na tsawon kwanaki 14 wanda shine tsarin daukar mataki.
Gwamnan jahar Gombe, Muhammad Yahaya, ya koka kan rashin iya biyan ma’aikata N30,000 a matsayin mafi karancin albashi da gwamnatinsa ta kasa.
Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun kashe mutum biyu a wani hari da suka kai kan al’umman kauyen Kujemi a masarautar Dansadau da ke karamar hukumar Maru na jahar Zamfara.
Wani tsohon hadimi na musamman ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jahar Kano kan kawata birane, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya ce bai yi danasanin yasar da tsohon ubangidansa da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba.
Aisha Musa
Samu kari