An sha kallo yayinda aka hana hadiman Oshiomhole shiga sakatariyar APC

An sha kallo yayinda aka hana hadiman Oshiomhole shiga sakatariyar APC

- Jami’an tsaro sun hana wasu hadiman Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole shiga sakatariyar jam’iyyar

- Hakan ya kasance ne duk da cewar an gane matsayinsu ta hanyar katin shaidarsu

- An kuma gano kugiyar ma’aikatan da ke adawa da Oshiomhole ma a tsaye suna kallon duk diramar da ke wakana a sakatariyar

Rahotanni sun kawo cewa jami’an tsaro sun hana wasu hadiman Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole shiga sakatariyar jam’iyyar.

An hana ma’aikatan wadanda suka isa wajen cikin wata mota kirar Toyota Jeep baka shiga sakatariyar duk da cewar an gane ko wanene su.

Jami’an tsaron sun bukace su da su bar wajen kofar shiga ofishin jam’iyyar.

An sha kallo yayinda aka hana hadiman Oshiomhole shiga sakatariyar APC
An sha kallo yayinda aka hana hadiman Oshiomhole shiga sakatariyar APC
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an gano ma’aikatan da ke adawa da Oshiomhole ma a tsaye suna kallon duk diramar da ke wakana a sakatariyar.

KU KARANTA KUMA: An yanke wa wani bawan Allah hukuncin kisa ta hanyar rataya a Kano

A baya mun ji cewa Shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Kwamared Adams Oshiomole ya bayyana dalilin da yasa wasu yayan jam’iyyar APC wadanda yake kallonsu a matsayin makiyansa suke kokarin tsige shi daga kujerar shugabancin jam’iyyar.

Daily Trust ta ruwaito Oshiomole ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru jim kadan bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnatin Najeriya a ranar Alhamis.

Wannan jawabi na Oshiomole ya zo ne jim kadan bayan wata babbar kotun tarayya dake zamanta a jahar Kano ta soke dakatarwar da wata babbar kotun babban birnin tarayya Abuja ta yi masa a ranar Laraba.

A cewarsa, ya kai ziyarar ne domin bayyana ma shugaban kasa halin da ake ciki a tirka tirkar da ta dabaibaye jam’iyyar APC, sa’annan yace akwai wani minista a gwamnatin shugaba Buhari da wasu gwamnoni dake shirya masa duk wani bita da kulli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng