Bana shirin karban mulki daga hannun Buhari - Fayemi

Bana shirin karban mulki daga hannun Buhari - Fayemi

- Gwamna Kayode Fayemi na jahar Ekiti ya karyata rade-radin cewa yana aiki don ganin ya karbi mulki daga hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023

- Fayemi ya ce sam shi baya daga cikin jerin masu neman wannan kujera ta shugaban kasa a 2023

- Ya ce shi mutum ne mai son ganin zaman lafiya shiyasa ya dukufa wajen yin sulhu da kawo zaman lafiya a tsakanin mutane

Gwamnan jahar Ekiti, Kayode Fayemi, ya ce ayyukansa ba yunkuri ne na karban mulki daga wajeen Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.

Da yake magana ta hannun babban mai bashi shawara na musamman kan jawabai ga jama’a, Segun Dipe, Fayemi ya ce baya daga cikin jerin wadanda ke aiki domin zama Shugaban kasa na gaba.

Ya bayyana lamarin a matsayin kanzon kurege, cewa yana aiki tukuru don ganin ya gina mizanin da zai gurfanar da “kudirinsa na neman shugabancin kasa a 2023 da ake ta rade-radi.

Bana shirin karban mulki daga hannun Buhari - Fayemi

Bana shirin karban mulki daga hannun Buhari - Fayemi
Source: Depositphotos

“Fayemi ya kasance gwamna ne mai ci kuma shine ke shugabantar kungiyar gwamnonin Najeriya. Yana jin dadin wadannan matsayin da yake kai sosai,” in ji jawabin.

“Manufarsa shine shiga tsare-tsare kamar yin sulhu, da shiga tsakani domin ganin an sasanta tsakanin mutane ta hanyar sulhu ba rikici ba.

KU KARANTA KUMA: Dakatar da Oshiomhole: Ayyuka sun tsaya cak a sakatariyar APC na kasa

“Yana da ra’ayi kan abubuwan da ke wakana a dukkanin yankunan kasar, kamar yadda ya taba furtawa da bakinsa, cewa duk wani abu da ya shafi kowace jaha da mamba na kungiyar gwamnonin Najeriya ke jagoranta zai shafi kungiyar ma.

“Mutane irin Fayemi na kawo hadin kan jama’a. Ana samun su a kowani irin wuri kuma a kowani irin yanayi. Sun kasance mutane abun soyuwa da ke sowa sauran mutane abu mai kyau. Duk da cewar aikinsa na kawo zaman lafiya da sulhu ya kasance babban abu a wajen sauran mutane, gwamnan ya kasance mutum mai mutunci wanda ya mayar da hankali ga farin cikin sauran mutane."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel