Oshiomhole zai san makomarsa yayinda APC ta kira taron gaggawa a tsaka da rikicin cikin gidanta

Oshiomhole zai san makomarsa yayinda APC ta kira taron gaggawa a tsaka da rikicin cikin gidanta

- Jam'iyyar mai mulki ta kira wani taron gaggawa na masu ruwa da tsaki

- Za a gudanar da taron ne a ranar Talata, 17 ga watan Maris, 2020 a babbar birnin tarayya Abuja

- An tsara za a gudanar da taron da karfe 3:00 na rana a dakin taro a sakatariyar jam’iyyar na kasa

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta kira wani taron gaggawa na masu ruwa da tsaki, wanda za a gudanar a ranar Talata, 17 ga watan Maris, 2020 a Abuja.

A wani jawabi daga mukaddashin sakataren jam’iyyar na kasa, Victor T. Giadom a Abuja a daren ranar Juma’a, 6 ga watan Maris, ya gayyaci dukkanin mambobin NEC da su halarci taron gaggawan kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Oshiomhole zai san makomarsa yayinda APC ta kira taron gaggawa a tsaka da rikicin cikin gidanta

Oshiomhole zai san makomarsa yayinda APC ta kira taron gaggawa a tsaka da rikicin cikin gidanta
Source: UGC

An tsara za a gudanar da taron da karfe 3:00 na rana a dakin taro a sakatariyar jam’iyyar na kasa da ke Abuja.

Sanarwar ta bukaci dukkanin mambobin kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da su kasance a zaune kafin zuwan Shugaban kasar.

An kira taron ne a tsaka da rikicin da ake fama dashi a jam'iyyar tun bayan da wata kotun tarayya ta dakatar da shugaban jam'iyyar Adams Oshiomhole. Ana kuma sanya ran dakataccen shugaban zai san makomarsa.

A baya mun ji cewa Shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Kwamared Adams Oshiomole ya bayyana dalilin da yasa wasu yayan jam’iyyar APC wadanda yake kallonsu a matsayin makiyansa suke kokarin tsige shi daga kujerar shugabancin jam’iyyar.

Daily Trust ta ruwaito Oshiomole ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru jim kadan bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnatin Najeriya a ranar Alhamis.

KU KARANTA KUMA: Toh fah: Jam’iyyar PDP ta sallami kaso 50 na ma’aikata a sakatariyarta

Wannan jawabi na Oshiomole ya zo ne jim kadan bayan wata babbar kotun tarayya dake zamanta a jahar Kano ta soke dakatarwar da wata babbar kotun babban birnin tarayya Abuja ta yi masa a ranar Laraba.

A cewarsa, ya kai ziyarar ne domin bayyana ma shugaban kasa halin da ake ciki a tirka tirkar da ta dabaibaye jam’iyyar APC, sa’annan yace akwai wani minista a gwamnatin shugaba Buhari da wasu gwamnoni dake shirya masa duk wani bita da kulli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel