APC na kara rushewa yayinda jam’iyyar ta yi watsi da hukuncin kotun Kano da ta soke dakatarwar da aka yi wa Oshiomhole

APC na kara rushewa yayinda jam’iyyar ta yi watsi da hukuncin kotun Kano da ta soke dakatarwar da aka yi wa Oshiomhole

- Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa, Salihu Mustapha ya ce kotun daukaka kara ce kadai za ta iya dawo da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyyar

- Ya bayyana hakan yayin da yake martani ya umurnin Justis Lewis Allagoa na babbar kotun jahar Kano wanda ya dawo da Osiohole kan kujerarsa

- Ya ce daga babbar kotun Kano da babbar kotun Abuja suna a hurumin daidaita tsakani ne

Mataimakin shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa daga yankin arewa maso gabas, Salihu Mustapha ya kaddamar da cewar kotun daukaka kara ce kadai za ta iya dawo da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.

Ya bayyana hakan yayin da yake martani ya umurnin Justis Lewis Allagoa na babbar kotun jahar Kano wanda ya soke wani umurni da Justis Danlami Senchi ya yanke da farko, wanda ya bukaci shugaban APC na kasa Adams Oshiomhole da ya sauka daga kujerarsa.

APC na kara rushewa yayinda jam’iyyar ta yi watsi da hukuncin kotun Kano da ta soke dakatarwar da aka yi wa Oshiomhole
APC na kara rushewa yayinda jam’iyyar ta yi watsi da hukuncin kotun Kano da ta soke dakatarwar da aka yi wa Oshiomhole
Asali: UGC

Da yake zantawa da manema labarai, Mustapha ya ce lallai kotun daukaka kara ce kadai za ta iya soke umurnin Justis Senchi, inda ya ce daga babbar kotun Kano da babbar kotun Abuja suna a hurumin daidaita tsakani ne.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Minista da wasu gwamnoni suka shirya tuggun dakatad da ni - Oshiomole bayan ganawarsa da Buhari

A baya mun ji cewa wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke jihar Kano ta jingine hukuncin babbar kotun tarayya da ke Abuja na dakatar da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adam Oshiomhole, a ranar Laraba.

A hukuncin da kotun ta yanke ranar Alhamis, mai shari'a, Jastis Lewis Allagoa, ta umarci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da rundunar 'yan sanda (NPF) a kan su mayar wa da Oshiomhole jami'an da ke tsaron lafiyarsa domin ya koma ofishinsa.

A ranar Labara ne mai shari'a, Jastis Danlami Senchi, ya bayar umarnin wucin gadi na dakatar da Oshiomhole daga gabatar da kansa a matsayin shugaban APC na kasa.

Sa'o'i kadan bayan zartar da hukuncin kotun a ranar Laraba, Oshiomhole ya daukaka kara zuwa wata kotun daukaka kara da ke Abuja.

Sai dai, har yanzu ba a samu cikakken rahoto a kan waye ya shigar da kara a kotun Kano dangane da dakatar da Oshiomhole ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel