Yanzun-nan: Buhari ya amince da nadin Jastis Mensen a matsayin madadin Jastis Zainab Bulkachuwa

Yanzun-nan: Buhari ya amince da nadin Jastis Mensen a matsayin madadin Jastis Zainab Bulkachuwa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Justis Monica B. Dongban Mensem a matsayin shugabar rikon kwarya a kotun daukaka kara

- Mensem za ta zama madadin Jastis Zainab Bulkachuwa wacce za ta yi ritaya a ranar 6 ga watan Maris

- Kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Justis Monica B. Dongban Mensem a matsayin Mukaddashin Shugaban kotun daukaka kara na tsawon watanni uku.

Nadin zai fara aiki ne nan take daga ranar 6 ga watan Maris, 2020, lokacin da shugaban kotun daukaka kara mai ci, Justis Zainab Bulkachuwa, Za ta yi ritaya daga aiki.

Yanzun-nan: Buhari ya amince da nadin Jastis Mensen a matsayin madadin Jastis Zainab Bulkachuwa

Yanzun-nan: Buhari ya amince da nadin Jastis Mensen a matsayin madadin Jastis Zainab Bulkachuwa
Source: UGC

A wata sanarwa daga mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu a Abuja a ranar Alhamis, 5 ga watan Maris ya bayyana cewa Justis Mensem, wacce ta kasance ta biyu a mukami a kotun daukaka karar za ta zama mukaddashin shugaba har zuwa lokacin da shugaba Buhari zai nada wanda zai cike gurbin sannan ya aike wa majalisar dattawa domin tabbatarwa.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Kotu a Kano ta jingine hukuncin dakatar da Oshiomhole a gefe

“Shugaban kasa ya amince da nadin Justis Mensem, biyo bayan shawarar shugaban alkalan Najeriya wanda ya yi daidai da sashi na 238(4) & (5) na kundin tsarin mulkin Najeriya kamar yadda aka gyara,” cewar sanarwar.

A wani labari na daban, mun ji cewa bayan ganawar sirri sakamakon sabanin da aka fara samu a zauren majalisa, Majalisar dattawan tarayya ta baiwa shugaba Muhammadu Buhari daman karbo bashin $23bn (dala bilyan 22,798,446,773).

Shugaba majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis bayan gajeren mujadalan da akayi kan hakan.

Yayinda ake muhawara kan lamarin, shugaban marasa rinjaye, Eyinnaya Abaribe, ya gargadi majalisar kan baiwa shugaban kasa daman karbo bashin duka kudaden a lokaci guda.

Ya bada shawaran cewa a tsara ta yadda zai rika karba daya bayan daya. Amma shugaban majalisar datawa ya bayyana rashin amincewarsa da hakan.

Bayan haka sai aka fara tafka muhawara kan lamarin har aka fara samun sabani kuma haka ya tilasta yan majalisar saka labule.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel