Yanzu Yanzu: Kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki

Yanzu Yanzu: Kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki

- Kungiyar malaman jami’a sun shiga yajin aiki karo na farko a 2020

- Yajin aikin wanda zai shafe tsawon makonni biyu ya fara ne daga ranar Litinin, 9 ga watan Maris

- Hakan ya biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya wajen cika alkawarin da ta daukar masu

Kungiyar malaman jami’a ta ASUU sun shiga yajin aikin jan kunne na makonni biyu daga ranar Litinin, 9 ga watan Maris.

Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi ne ya sanar da hakan a karshen taron kwamitin masu ruwa da tsaki na kungiyar wanda aka gudanar a jami’ar kimiya da fasaha na jahar Enugu (ESUT).

Yanzu Yanzu: Kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki

Yanzu Yanzu: Kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki
Source: Depositphotos

Ogunyemi ya ce yajin aikin ya kasance matakin tursasa gwamnatin tarayya domin ta aiwatar da yarjejeniya da shawarar da aka yanke a tattaunawar da aka yi tsakanin kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya a 2009, yarjejeniyar 2013 da na 2017 wanda duk aka ki aiwatar dasu.

KU KARANTA KUMA: Yanzun-nan: An tabbatar da mutum na biyu da ke dauke da coronavirus a Najeriya

A wani lbarin, mun ji cewa Ministar kudi da kasafin kudi ta ce duk lakcaran da bai yi rijista a manhajar biyan albashin bai daya na IPPIS ba zai samu albashin watan Febrairu da ya kare ba.

Yayinda take magana da manema labarai a Kano ranar Alhamis, ministar tace kashi 55 cikin 100 na mambobin kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU sun yi rijista a manhajar.

A watan Junairu, gwamnatin tarayya ta bada umurnin daina biyan lakcarori da dukkan ma’aikatan manyan makarantun gaba da sakandaren da ke Najeriya da suka ki rijista a manhajar IPPIS.

Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU ta lashi takobin tafiya yajin aiki idan basu samu albashinsu ba.

ASUU ta yi watsi da dukkan umurnin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikata na rijista saboda hakan zai rage musu karfi.

Amma, Zainab ta ce duk da cewa akwai taurin kai ta bangaren ASUU, manufar manhajar ita ce rage rashawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel