Yadda ‘Ririta’ Peter Obi a ADC Ya Kusa Tilasta wa Amaechi Barin Jam’iyyar

Yadda ‘Ririta’ Peter Obi a ADC Ya Kusa Tilasta wa Amaechi Barin Jam’iyyar

  • Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi ya yi magana game da zargin da ake yi kan Peter Obi a jam'iyyar
  • Bolaji ya bayyana yadda Rotimi Amaechi ya taba barazanar ficewa daga kawancen adawa saboda tsohon gwamnan
  • Ya ce Obi ya samu dama a tsarin kawance inda aka ba shi mukamai da dama wanda wasu ke ganin ana nuna wariya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi ya yi karin haske kan abin da ya kusa sanya Rotimi Amaechi barin jam'iyyar.

Bolaji ya yi bayanin cewa Amaechi ya taba barazanar ficewa daga kawancen adawa saboda fifita Peter Obi.

ADC ta bayyana yadda Amaechi ya yi barazanar barinta
Tsohon gwamnan Rivers kuma jogin ADC, Rotimi Amaechi. Hoto: Rotimi Amaechi Support Team, Mr Peter Obi.
Source: Facebook

Kakakin jam'iyyar ADC mai adawa ya bayyana haka yayin hira da yan jarida wanda TheCable ta bibiya.

Yadda Amaechi ya kalubalanci jam'iyyar ADC

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya fadi yadda Atiku ke rage masu wahala a zaben 2027

Ya ce Amaechi ya kalubalanci shugaban kawance kan fifita Obi, inda aka ba bangaren Obi mukamai ciki har da nadin wakilai da sauran mukamai.

A cewarsa, an ba Obi damar zaben wasu cikin jam’iyya, wanda ya haifar da rasa mukamin Osita Chidoka a tsarin kawance.

Ya ce:

"Akwai lokacin da Rotimi Amaechi ya je wajen shugaban ƙasa na jam’iyya yana barazanar zai fice daga kawancen.
“Ya ji cewa shugaban yana nuna fifiko ga Peter Obi, har ma yana miƙa masa komai da komai.”
ADC ta caccaki Obi kan dalilinsa na barin jam'iyyar
Tsohon gwamnan Anambra kuma jigon NDC, Peter Obi. Hoto: Mr Peter Obi.
Source: UGC

ADC ta dura kan Peter Obi, Kwankwaso

Bolaji ya mayar da martani ne game da ikirarin Peter Obi kan dalilin da ya sa suka bar ADC shi da Sanata Rabiu Kwankwaso, cewar Vanguard.

Ya ce Obi ya nanata cewa “rikice-rikicen cikin gida, shari’o’in kotu marasa adadi da rashin tabbas kan makomar jam’iyya” ne suka suka fice daga jam’iyyar zuwa NDC.

Tsohon ministan ya ce Peter Obi ba shi da hurumin da zai iya yin irin wannan ikirari kan ADC, ya ce ya samu gata da dama fiye da kowane shugaban haɗin gwiwar ‘yan adawa a lokacin da yake cikin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Bayan tadiye yaransa a tantancewar APC, Fubara ya magantu kan alakarsa da jam'iyya

Ya ce:

“Na kasance da mataimaka biyu a ƙarƙashina, kuma ɗaya daga cikinsu Peter Obi ne ya tsayar da shi. Amaechi da Atiku ba za su iya nuna ko mutum ɗaya da suka tsayar a cikin kwamitin zartarwa ba. Sakataren tsare-tsaren jam’iyya na ƙasa ma mutum ne na Peter Obi.
“Kafin Obi ya shiga haɗin gwiwar, muna da wasu mutane kamar Osita Chidoka da ke aiki tuƙuru wajen gina wannan haɗin gwiwa.”

Peter Obi ya sha alwashin yin wa'ada 1

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya nanata alkawarin da ya yi na yin zangon mulki daya idan aka zabe shi a shekarar 2027.

Obi, wanda ya koma NDC kwanan nan, ya ce ba zai kara awa guda a kan shekaru hudu ba ko da kuwa an sanya masa bindiga a kansa.

Wannan dai ba shi ne karon farko da tsohon gwamnan ke fadar hakan ba, ya ce kwashe tsawon lokaci a kan mulki ba shi ke kawo masara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.